Karin bayani: 'Yan bindiga sun harbe mai shayi, direba da 'yan kasuwa a jihar Ondo

Karin bayani: 'Yan bindiga sun harbe mai shayi, direba da 'yan kasuwa a jihar Ondo

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun farmaki mazauna wasu yankuna a jihar Ondo, sun hallaka mutane hudu
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an hallaka wani direba da kuma mai sayar da shayi a yankunan
  • Lamarin da ya tada hankali ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane hudu kamar yadda wata majiya ta shaida

Jihar Ondo - Wasu ‘yan bindiga da ke barna a kan babura sun harbe wasu mutane hudu da suka hada da masu sayar da shayi da wani direba da kuma ‘yan kasuwar gefen hanya har lahira.

Kisan ya faru ne a kusa da Sabo da Igba a cikin garin Ondo a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wata majiya ta ce wasu ’yan kungiyar asiri ne suka kai hari kan wata kungiyar asirin, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta karyata batun kai harin ramuwar gayya kan al’umman Hausawa a Ondo

Yadda 'yan bindiga suka hallaka mazauna a wani yankin Ondo
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun harbe mai shayi, direba da 'yan kasuwa a jihar Ondo | Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Wata majiyar kuma ta ce ba a san manufar ‘yan bindigar ba, yayin da suka yi ta harbe-harbe, inda suka kashe mutane uku a Sabo da kuma mutum daya a Igba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa, wani direban kasuwa da ya tsaya cin abinci a yankin an harbe shi shima har lahira, Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Ondo, SP Fumilayo Odunlami, ta ce za ta fitar da sanarwa bayan samun cikakkun bayanai.

Amma wata majiyar ‘yan sanda a garin Ondo ta tabbatar da faruwar kisan.

Majiyar ‘yan sandan ta ce ‘yan bindigar ‘yan fashi ne da suka yi yunkurin yin fashi ga mazauna da kuma ‘yan kasuwa a yankin.

Wata tattaunawa da sarkin Hausawan Ondo Alhaji Abdulsalam Yusuf, da Daily Trust ta yi, ya shaida cewa, 'yan bindigan sun hari yankin Hausawa ne tare da kashe su.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsageru sun sace mai daukar hoton gidan gwamnatin jiha, suna neman N50m

Sai dai, wani rahoton da jaridar Punch ta sake fitar ya ce, rundunar 'yan sadna ta karyata cewa Hausawa aka farmaka.

'Yan bindiga sun shiga Abuja da sanyin safiya, sun sace mutane da dama

A wani labarin, The Guardian ta ce, wasu tsageru da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a safiyar ranar Litinin sun kai hari a jerangiyar gidaje na Gwarinpa da ke babban birnin tarayya.

Daily Trust ta gano cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki a gidajen ne tsakanin karfe 1 na dare zuwa karfe 4 na asuba, inda suka yi awon gaba da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani, wani mazaunin garin, wanda kawai ya bayyana sunansa da Mohammed ya ce ‘yan bindigar sun samu shiga jerangiyar gidajen Genuine katin shiga na Efab Queens da ke 6th Avenue, Gwarinpa.

Kara karanta wannan

Samun wuri: 'Yan ta'addan IPOB sun banka wa motar siminti wuta a jihar Kudunci

Asali: Legit.ng

Online view pixel