Da dumi-dumi: Tsageru sun sace mai daukar hoton gidan gwamnatin jiha, suna neman N50m

Da dumi-dumi: Tsageru sun sace mai daukar hoton gidan gwamnatin jiha, suna neman N50m

  • Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani madaukin hotunan gidan gwamnatin Ebonyi
  • Wannan lamari ya faru ne a ranar 8 ga watan Yuni yayin da yake hanyarsa ta komawa Abakaliki ta jihar
  • Ya zuwa yanzu, ya shaida cewa, 'yan bindigan na neman akalla Naira miliyan 50 kafin su sako shi

Jihar Ebonyi - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da madaukin hoton gidan gwamnatin jihar Ebonyi, Mista Uchenna Nwube a hanyar Okigwe-Aba-Enugu.

Wannan lamari ya bude jerin tattaunawa tsakanin 'yan jarida da ma'aikatan gidan gwamnati game da lafiyar wanda aka sace, Vanguard ta ruwaito.

Madaukin hotunan da aka sace a Ebonyi
Da dumi-dumi: Tsageru sun sace mai daukar hoton gidan gwamnatin jiha, suna neman N50m | Hoto: abacityblog.com
Asali: UGC

Nwube, wanda masu garkuwa da mutane suka ba shi damar kira ta wayarsa, ya shaida wa wasu ‘yan jarida cewa an yi garkuwa da shi ne a ranar Laraba da misalin karfe 7 na dare, Pulse ta tattaro.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram sun farmaki Borno, sun sace fasinjoji masu yawan gaske

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“An sace ni ne a yau, 8 ga watan Yuni lokacin da nake dawowa Abakaliki daga Aba, kuma ina tare da wasu mutane a motata.
“A yanzu haka, su (masu garkuwa da mutanen) suna neman Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa, wanda ban san yadda ko ina zan samu irin wadannan kudade ba. Don Allah, ina bukatan taimako,”.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Ebonyi, SP Chris Anyanwu, ya shawarci wanda abin ya shafa da ya kwantar da hankalinsa ya lallabi tsagerun.

A cewar Anyanwu:

“Yankin da abin ya faru baya cikin ikonmu a Ebonyi. Wancan wurin yana tsakanin Imo da Abia ne."

Da dama dai na ganin ya kamata gwamnati mai ci ta hada karfi da karfe domin ganin an sako wanda aka sace, duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar.

Kara karanta wannan

Abinda aka yiwa Awolowo da Abiola ake kokarin yiwa Tinubu, Ayo Fayose

'Yan bindiga sun harbe mai shayi, direba da 'yan kasuwa a jihar Ondo

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga da ke barna a kan babura sun harbe wasu mutane hudu da suka hada da masu sayar da shayi da wani direba da kuma ‘yan kasuwar gefen hanya har lahira.

Kisan ya faru ne a kusa da Sabo da Igba a cikin garin Ondo a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wata majiya ta ce wasu ’yan kungiyar asiri ne suka kai hari kan wata kungiyar asirin, rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel