Harin jirgin ƙasan Kaduna: Yan bindiga sun sake gargaɗin gwamnati a sabon Bidiyo

Harin jirgin ƙasan Kaduna: Yan bindiga sun sake gargaɗin gwamnati a sabon Bidiyo

  • Yan ta'addan da suka farmaki jirgin ƙasa a Kaduna suka sace mutane sun sake aiko wa da sabon Bidiyo ga FG
  • Yan bindigan sun baiwa gwamnatin tarayya zaɓi biyu, ko ta saurari Fasinjojin da ke hannun su ko kuma ta manta da babin su
  • Wata daga cikin Fasinjojin da aka sace ta bayyana halin da suke ciki a sansanin yan ta'adda, ta roki a kawo musu ɗauki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Ɗaya daga cikin yan ta'addan da suka sace Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga watan Maris, ya ce gwamnatin tarayya na da zaɓi biyu, ko dai ta saurare fasinjojin ko ta mance babin su.

Daily Trust ta rahoto cewa ɗan ta'addan, wanda ya rufe fuskarsa, ya faɗi hakane a wani sabon Bidiyo, wanda ya nuna nutum 8 daga cikin fasinjojin na rokon FG ta kawo musu ɗauki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Ɗan Ango Abdullahi, 'yar ajinsu Osinbajo sun yi magana a sabon bidiyon da ƴan ta'adda suka saki

Harin jirgin ƙasan Kaduna.
Harin jirgin ƙasan Kaduna: Yan bindiga sun sake gargaɗin gwamnati a sabon Bidiyo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mutumin wanda ya yi magana cikin harshen turanci, ya ce:

"Mune mutanen da suka sace Fasinjoji daga jirgin ƙasar Kaduna-Abuja, suna ta rokon mu da cewa suna bukatar mu ba su dama su yi magana da gwamnatin tarayya."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Saboda haka yanzu mun ba su dama su yi magana, daga nan ya rage gare ku, ku saurare su ko kuma ku mance da su."

Wace magana Fasinjojin suke son yi?

Ɗaya daga cikin mutanen da ke hannun yan ta'addan wacce ta bayyana sunanta da Mariam Abubakar, ta ce 'ya'yanta sun kamu da rashin lafiya a sansanin yan bindiga.

A kalamanta na cikin Bidiyon ta ce:

"Ina daga cikin fasinjojin da aka sace a jirgin ƙasa tare da iyalaina hudu da kuma Mijina, muna rokon gwamnatin tarayya, yan uwan mu da duk wanda yake tausaya mana su kawo mana agaji."

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji

"Mun kwashe kwanaki 62 a wurin nan, mun kwanta rashin lafiya, biyu daga cikin ƴaƴana ba su da lafiya tare da babu mai kula da lafiyarsu. Saboda haka muna rokon ku kawo mana ɗauki."

Iyalan Fasinjojin da aka sace sun jima suna kiran gwamnatin tarayya ta kuɓutar da yan uwansu, yayin da a bangarenta FG ta tabbatar da cewa tana ɗaukar matakan da ya dace na kuɓutar da su.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun halaka tsohon kwamishinan NPC, sun sace 'ya'yansa mata

Yan bindiga sun kutsa gidan tsohon kwamishinan NPC ta ƙasa, sun kashe shi kuma sun yi garkuwa da 'ya'yansa mata biyu.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun shiga gidan da tsakar dare, sun nemi a ba su miliyan N50m kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel