Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji

Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji

  • An gano inda 'ya'ya takwas na 'yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suke kuma an nuna wa 'yan ta'addan hotunansu
  • Mai magana da yawun Gumi, Tukur Mamu, ya sanar da cewa sun gano su tare da taimakon jami'an tsaron jihar Adamawa
  • Mamu ya sanar da cewa, 'yan ta'addan sun kara wa'adin mako 1 kan wa'adin farko da suka bayar, sun kuma samu natsuwa ganin cewa 'ya'yansu 8 na da rai
  • Ana sa ran mika musu 'ya'yansu kafin ranar 13 ga watan Yuni sannan su sako fasinjojin da ke hannunsu karkashin Abu Barra, shugaban 'yan ta'addan

Kaduna - 'Yan ta'addan da suka kai wa jirgin kasan Kaduna hari sun kara sati biyu a kan wa'adin barazanar halaka fasinjoji 62 da har yanzu suke hannunsu yau, rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

Sai dai, sharadin jinkirin shi ne: Wajibi ne gwamnatin tarayya ta sakar musu yaransu takwas dake hannunsu kafin ko ranar 13 ga watan Juni daga nan ne za a cigaba da maganar sakin fasinjoji 62.

Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji
Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

A ranar 28 ga watan Maris ne 'yan ta'addan suka halaka fasinjoji tara gami da garkuwa da mutane da dama bayan lalata jirgin kasa a wani kilomita kadan daga Kaduna, babban birnin jihar Kaduna. Daga bisani sun sako wasu daga ciki, tare da barin 62 a hannunsu.

Wani mawallafi mazaunin Kaduna, Tukur Mamu, ya bayyana karin mako daya na wa'adin ranar da masu garkuwa da mutanen su ka yi a Talatar da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mamu, wanda kuma shi ne mai magana da yawun fitaccen malamin addinin musuluncin da ya dade yana jawo cece-kuce, Sheikh Ahmad Gumi, wanda bai ce uffan ba a lokacin da gwamnatin tarayya tayi awon gaba da kananan yaran 'yan ta'addan takwas.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja

Mamu ya ce ya yi nasarar rarrashin 'yan ta'addan har suka jinkirta wa'adin kwanakin da suka bayar bayan an gano inda yaran nasu suke tare da taimakon hukumomin tsaro na jihar Adamawa.

A cewar marubucin, ba alkawarin cigaba da ciyar da wadanda suka yi garkuwan da su kadai suka yi ba har da kiyaye kiwon lafiyarsu.

An yi wannan nasarar ne bayan 'yan ta'adda karkashin Abu Barra, sun ga hotunan yaran da aka kwace musu a hotunan da aka nuna musu.

Ta bakin nashi:

"Kai tsaye zan iya tabbatar da cewa sun janye barazanar da suka yi da farko na daina ciyar da fasinjojin da su ka yi garkuwan da su a jirgin kasan Abuja-Kaduna tare da barazanar fara halaka su a ranar Lahadi."

Ya cigaba da cewa:

"Hakan sakamakon tattaunawa da mabiyan Abu Barra ne. Wannan babban cigaba ne, duk lamurran da suka shafi tsaron rayukan wadanda lamarin ya ritsa dasu ne, don tabbatar da cigaba da kasancewa da masu garkuwa da mutane tare da samun natsuwa, ba za mu yi sakaci da wannan cigaban ba wanda ya zo kasa da awanni 48 bayan masu garkuwa da mutanen sun saki wani bidiyon barazana ga wadanda suka yi garkuwan da su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan

"Mun yi kokarin gano inda yaran takwas suke tare da goyon bayan hukumomin tsaro, inda daga bisani muka tabbatar musu da yaransu na da rai, wanda cigaban ya taimaka wajen samun natsuwa,"
"Saboda irin gaskiyar da muka nuna musu yasa suka amince za su cigaba da kula da wadanda aka yi garkuwan da su tare da kula da lafiyarsu wanda a cewarsu sun dauki tsawon lokaci suna yi.
"A ra'ayina na amincewa da nema musu 'yanci kawai saboda jin kai ne kuma tare da sadaukarwa da jajircewar Sheikh Ahmad Gumi don ta kawo zaman lafiya mai dorewa a arewa, musamman arewa maso yamma," yace.

'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja

A wani labari na daban, iyalan fasinjojin da aka sace yayin da suke kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun balle zanga-zanga a babban birnin tarayya ta Abuja.

Wannan ne karo na farko da 'yan uwan wadanda aka sacen suka fito zanga-zanga tun bayan faruwar ibtila'in, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

A ranar 28 ga watan Maris din 2022, 'yan ta'adda sun kai mugun hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna kuma hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum takwas yayin da 26 suka jigata kuma aka yi garkuwa da wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel