Hotuna: Buhari tare da uwargidansa sun dawo Najeriya daga taron da suka halarta a Malabo
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Aisha Buhari sun iso Najeriya bayan halatar taron AU da suka yi Malabo, Equitorial Guinea
- A yayin taron, Buhari ya sha alwashin gwangwaje kungiyar taimakon kai da kai da AU ta kafa da kudi har $3 miliyan
- Ya bayyana tsagwaron goyon bayansa ga hukuma tsaron da aka shawarta kafawa a Afrika domin yaka ta'addanci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari tare da uwargidansa, Aisha Buhari, a ranar Asabar sun dawo gida Najeriya bayan halarta gagarumin taron kungiyar hadin kan Afrika da aka yi a Malabo, Equitorial Guinea.
Shugaban kasan ya ziyarci Malabo domin halartar taro kashi na 16 na kungiyar hadin kan Afrika kan ta'addanci da tashin-tashina a Afrika.
A yayin taron, Buhari ya yi alkawarin kyautar $3 miliyan ga sabuwar cibiyar da kungiyar hadin kan Afrika ta kafa.
Shugaban kasan ya kara da bayyana goyon bayansa kan shawarar da aka yi ta kafa wata hukumar tsaro ta yaki da ta'addanci a Afrika, The Cable ta ruwaito..
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng