Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Osinbajo Kafin Ya Tafi Kafin Ya Shilla Birnin Malabo

Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Osinbajo Kafin Ya Tafi Kafin Ya Shilla Birnin Malabo

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo kafin ya tafi Malabo taron Kungiyar Hadin kan Afirka, AU
  • Duk da cewa ba a sanar da abin da shugaban kasar ya tattauna da mataimakinsa ba a yanzu, ana kyautata zaton sunyi magana kan zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa na APC
  • Ana fatan Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya ranar jajiberin ranar fara tantance yan takarar shugaban kasar na APC gabanin zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya gana da mataimakinsa Yemi Osinbajo jim kadan kafin tafiyarsa zuwa Malabo, Equatorial Guinea don hallartar taron AU.

Buhari Sallau, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hakan cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba

Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Osinbajo Kafin Ya Tafi Kafin Ya Shilla Birnin Malabo
Buhari Ya Gana Da Osinbajo Kafin Ya Tafi Kafin Ya Shilla Birnin Malabo. Hoto: Buhari Sallau.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar hadin kan Afirkan, AU, za ta yi tarurukanta ne daga ranar 25 zuwa 28 na watan Mayu shekarar 2022 kamar yadda The Cable ta rahoto.

Ana kyautata zaton Buhari da Osinbajo sun tattauna game da zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa a APC da ke tafe

Taron tsakanin Buhari da mataimakinsa wanda aka yi a ofishin shugaban kasar tana zuwa ne a lokacin da jam'iyyarAPC ke shirye-shiryen yin zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa da za a yi daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Mayu.

Duk da cewa ba a sanar da abin da aka tattauna a taron ba a hukumance kawo yanzu, The Cable ta fahimci cewa cikin abin da aka tattauna akwai batun zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa da ke tafe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

A cewar majiyoyi, ana fatan shugaban kasar zai dawo Najeriya ranar jajiberin zaben fidda gwanin na yan takarar shugaban kasar na APC.

Har yanzu, Shugaba Muhammadu Buhari bai riga ya bayyana dan takarar shugaban kasa da ya ke son ya gaje shi ba, amma wasu majiyoyi sun ce 'yana da wahala mataimakin shugaban kasar ya fito takarar ba tare da samun goyon bayan maigidansa ba.'

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa ya gana da Jonathan gabannin zaben fidda magajin Buhari

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel