Ban taba tunani a raina zan zama Sarki ba - Nasir Ado Bayero

Ban taba tunani a raina zan zama Sarki ba - Nasir Ado Bayero

  • Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero ya kasance 'da ga marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero
  • A wata tattaunawa da aka yi da shi, Sarkin na Bichi ya bayyana yadda ya taso a gidan sarauta har kawo yanzu
  • Ya kuma bayyana cewa bai taba tunanin zai zama sarki ba a rayuwarsa

Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero ya kasance daya daga cikin ‘ya’yan marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

A wata hira ta musamman da jaridar Daily Trust tayi da shi, Sarkin Bichi ya bayyana yadda ya taso a gidan sarauta.

Ban taba tunani a raina zan zama Sarki ba - Nasir Ado Bayero
Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero ya ce bai taba sawa a rai cewa zai zama Sarki ba Hoto: Maikatanga
Asali: Facebook

Yace ba a bashi wata kulawa ta musamman a matsayinsa na Yarima domin ya taso ne cikin bayi kuma babu wani banbanci tsakaninsa da yaransu.

Ya kuma bayyana cewa bai taba tunanin zai zamo sarki ko hakimi ba domin ba wannan bane matsalarsa, illa kawai ya ce yana son ganin ya yi wani abin a-zo-a-gani a rayuwarsa domin ya kawo ci gaba a rayuwar mutane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da mai tambayar da ya fara da son jin labarin rayuwarsa, Sarki Nasir ya ce:

“Ba lallai ba ne na iya tuna komai game da farkon rayuwata ba. Amma zan iya tuna cewa na taso ina da kusanci sosai da mahaifina.
“A matsayina na saurayi a cikin fada, a zahiri na girma kusa da shi. Na girma a gadonsa. Na taso tare da shi har zuwa lokacin da na fara karatu a makarantar sakandare.
“Zan iya tuna akwai wasu lokuta da nake makarantar firamare lokacin da nake buya in gudu kan gadonsa in yi barci. Nakan taimaka masa wajen daura rawaninsa. Don haka, na san shi sosai. Wannan shi ne tushen ilhamar da na samu a rayuwata daga mahaifina.
“Ba a taba dauka ta a matsayin wani yarima ba. Na taso tare da bayi a fada, da ni da sauran yara ba wani bambanci. Ban taba samun wata alaka ta musamman ko wata kulawa ta musamman ba kuma hakan ya yi tasiri sosai game da halayena a yau."

Sarkin na Bichi ya kuma bayyana cewa ya kan ji rashin dadi a ransa idan ya tuna da mahaifinsa.

Hakazalika da aka tambaye shi kan yadda ya ji a lokacin da bai samu darewa kujerar mahaifinsa ba duba ga yadda mutane suka dunga hasashen ko shi zai iya gadarsa, sai ya ce:

“Nufin Allah ne. Haka Allah Ya so. Ban taba tunanin zan zama Sarki ba. Bai taba zama wani buri a wajena ba.
"Haka ne, ina son in yi nasara. Tabbas, ina son in zama mutum mai nasara amma ba ni da burin zama Sarki ko hakimin gunduma ko wani abu.
"Ina so in yi wani abin a-zo-a-gani a rayuwata. Ka aikata wa mutane alheri don ci gaba. Don haka, kasancewar ni ba Sarki ba ne lokacin bai sa ni jin wani bambanci ko bakin ciki ba, ko kadan. Nufin Allah ne ba wanda zai iya canja haka."

Game da yadda ya ji a lokacin da aka nada shi sarautar Sarkin Bichi, ya ce:

“Yanayin ya kasance iri daya kamar yadda nake ji a baya. Tabbas kamar yadda na ce, ina son rayuwa cikin natsuwa.
“Za a ji kamar wani iri in ce, na girma a cikin gidan sarauta amma kuma ina son rayuwa ni kadai, wannan shi ne matsayata.
“Don haka, sake zama Sarki a yanzu a wannan lokaci nufi ne kawai na Allah, kawai dama ce na yi aiki don yin hidima ga al’umma.”

Na so diyata ta kammala karatunta kafin aure, Sarkin Bichi kan shirin auren diyarsa da Yusuf Buhari

A wani labarin, mun kawo cewa mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya bayyana cewa ya so ’diyarsa, Zahra Bayero, ta kammala karatunta kafin tayi aure.

Zahra Bayero dai za ta auri 'dan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A tattaunawar Sarkin Bichi da jaridar Aminiya, mai martaba ya bayyana yadda yake yanzu da zai aurar da diyarsa zahra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel