Wata Sabuwa: Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

Wata Sabuwa: Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

  • Gabanin babban zaben shekarar 2023, shahararren lauya Femi Falana, SAN, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya sake yin takara ba
  • Falana ya ce sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulki ta hana tsohon shugaban kasar sake yin takarar shugaban kasa a 2023
  • Kalaman na babban lauyan na zuwa ne a lokacin da ake hasashen Jonathan zai fice daga PDP ya koma APC don yin takarar shugaban kasa

Jihar Lagos - Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

An ba Jonathan kwanaki 7 ya shiga APC, ya fito takarar Shugaban kasa da karfi-da yaji

2023: Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba, Falana Ya Bada Hujja
2023: Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba, Falana Ya Kawo Hujja a Kudin Tsarin Mulkin Kasa. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

An zabi Jonathan a matsayin shugaban kasa a 2011 amma a shekarar 2015 ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Falana, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce:

"An tabbatar cewa tsohon shugaban kasar zai koma jam'iyyar APC domin yin takara a zaben shugaban kasa na 2023.
"Amma, sashi na 137 (3) na kudin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 kamar yadda aka yi mata gyaran fuska ta hana shi takarar: sashin ya ce duk mutumin da aka rantsar da shi ya karasa wa'adin wani mutum, sau daya kawai za a iya zabensa a wannan kujerar."

Abin Da Maƙarfi, Fayose, Da Wasu Shugbannin PDP Suka Ce Game Da Ƙishin-Ƙishin Ɗin Komawar Jonathan Zuwa APC

Kara karanta wannan

2023: Osinbajo Ya Gama Biyan Sadaki, Ya Cancanta Ya Zama Sabon Angon Nigeria, In Ji Basaraken Ƙasar Yarbawa

A yayin ake cigaba da yada jita-jitar cewa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan zai fice daga Jam'iyyar PDP ya koma APC, kawo yanzu APC bata ce komai ba; shugabannin jam'iyyar adawar ta PDP a ranar Talata sun yi magana da Vanguard game da batun.

Jonathan wanda aka zabe shi shugaban kasa a 2011 amma ya sha kaye hannun Muhammadu Buhari a 2015, ya juya wa PDP baya cikin shekaru bakwai da rabi da suka shude.

Ya rika kauracewa tarurukan jam'iyyar har da taronsu na kasa a 2017, 2018 da na 2021 inda aka zabi shugabannin jam'iyyar da ke rike mu madafan iko a yanzu da wasu tarukan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel