Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba

Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba

  • Gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC, shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu ya magantu kan halin da ake ciki
  • Adamu ya bayyana cewa ba lallai bane tsarin tsayar da dan takara na maslaha ya yiwu kamar yadda aka yi wajen zabar shugabannin jam'iyyar a watan Maris
  • Ya ce su dai abun da za su yi a matsayinsu na shugabanni shine tabbatar da gaskiya da kuma zabar wanda ya cancanta domin daga tutarsu a zaben

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda za a fara a ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ba lallai bane tsarin maslaha da aka yi amfani da shi wajen zaban shugabannin jam’iyyar a watan Maris ya yi aiki.

Kara karanta wannan

LP, NNPP, Jam’iyyu 4 da Peter Obi zai iya komawa kafin zaben 2023 bayan watsi da PDP

A wata hira da ya yi da muryar Amurka a Abuja a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, Adamu ya ce zaben fidda dan takarar shugaban kasa ya sha banban sosai da na zaben shugabancin jam’iyyar.

Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba
Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba Hoto: APC
Asali: Facebook

Ya ce:

“Kujerar shugaban jam’iyya ba daya bane da na shugabancin kasar. Ba ma za ka iya kwatanta biyun ba. Wannan tambayar bata taso ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Sai dai kuma jam’iyyar ta shimfida dokoki da ka’idojinta ga yan takara. Za mu binciki dukkan su bisa ka’idojinmu don tabbatar da ganin cewa mun zabawa jam’iyyar wanda ya dace.”

Ya kuma bayyana cewa ya kamata masu neman takarar 28 su san cewa dukkaninsu ba za su iya bayyana a matsayin dan takarar jam’iyyar da ta tsayar ba, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce:

“Ba za ka iya hana wani jigon jam’iyya yin takarar zabe ko neman shugabancin kasa ba. Hakkinsu ne kuma muna masu murna. Babu laifi wani ya nemi kujerar shugaban kasa. Allah ne ke tsara duk abun da mutum zai samu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

“Da zaran Allah ya yanke hukunci sannan ya ce ga wanda yake so, shine abun da muke roka. Muna da masu takara 28 da ke neman tikitin shugaban kasa kuma kowa ya san cewa dukkaninsu ba za su iya samun tikitin ba.
“Idan nufin Allah ne dukkansu suna iya zama shugaban kasar daya bayan daya. Namu shine tabbatar da adalci wajen zabar wanda zai zama dan takarar jam’iyyar. Hakan ba yana nufin mu kwararru bane. Amma muna addu’a mu aikata abun da yake daidai.”

Shugaban APC na kasa ya gana da Jonathan gabannin zaben fidda magajin Buhari

A wani labarin, mun ji cewa shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sake ganawa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki da za a yi a ranar Lahadi, jaridar Punch ta rahoto.

An tattaro cewa ganawar tasu ta riga tattaunawar da ya wakana tsakanin Jonathan da Mamman Daura, dan uwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

An rahoto cewa Jonathan da Adamu sun gana ne a gidan tsohon shugaban kasar da ke Abuja a makon da ya gabata kuma sun shafe kimanin awanni hudu a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel