An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

  • Bayan tsaikon da aka samu a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Neja, an samu babban abin takaici da ya faru
  • An ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun hallaka deliget uku na jam'iyyar PDP da suka halarci taron zaben
  • Hakazalika, wani wanda ya kubuta daga harin 'yan bindigan ya bayyana yadda lamarin ya faru da kuma yadda ya kubuta

Jihar Neja - Wasu ‘yan bindiga sun kashe deliget-deliget uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kwamitin zabe kuma mataimakin gwamnan jihar Bayelsa Lawrence Ewhrudjakpo ne ya sanar da haka a sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar, wurin da aka gudanar da zaben fidda gwanin.

An hallaka deliget-deliget na PDP a jihar Neja
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun harbe deliget-deliget na PDP a jihar Neja | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An ce an kashe su ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da suke komawa Mariga bayan da jam’iyyar ta dage zaben fidda gwanin sakamakon zanga-zangar da wasu ‘yan takara suka yi da nuna rashin amincewa da jerin sunayen wasu deliget din.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi garkuwa da 'yar takarar APC ana tsaka da zaben fidda gwani

Daga nan ne aka bukaci da su kawo shaidan tantance sunayensu don tantance bayanasu a zaben fidda gwanin da aka canja zuwa ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sauya wadanda suka rasa rayukansu a lamarin domin cike adadin deliget daga karamar hukumar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sakamakon haka, daya daga cikin deliget din, Shehu Haruna ya shaida wa Daily trust cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Mariga da Tegina kuma mutane hudu sun rasa rayukansu.

A cewarsa:

“Mun bar Minna ne cikin kurarren lokaci bayan da PDP ta dage zaben fidda gwani na gwamna zuwa ranar Alhamis, cewa mu je mu kawo katin zabe ko kuma wata hanyar ta tantance ingancinmu.
“Muna komawa gida ne domin dauko bayananmu, kuma a kan hanya muka ci karo da ‘yan bindigar da suka bude wa motar mu wuta. Ko da yake mun iya tserewa tunda ba a harbi direban ba, amma mutane hudu sun mutu nan take.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

Ya ce karamar hukumar ta su da ke kan iyaka da Birnin-Gwari a Kaduna ta zama maboyar ‘yan bindiga da ke aikata ta’addanci akai-akai.

Haruna ya yi kira da a samar da jami’an tsaro na dindindin a yankin da su kare matafiya da al’ummomin yankin.

Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba

A wani labarin, gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, wanda za a fara a ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ba lallai bane tsarin maslaha da aka yi amfani da shi wajen zaban shugabannin jam’iyyar a watan Maris ya yi aiki.

A wata hira da ya yi da muryar Amurka a Abuja a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, Adamu ya ce zaben fidda dan takarar shugaban kasa ya sha banban sosai da na zaben shugabancin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Akanta janar din jihar Ribas ya lashe tikitin gwamnan PDP

Ya ce: “Kujerar shugaban jam’iyya ba daya bane da na shugabancin kasar. Ba ma za ka iya kwatanta biyun ba. Wannan tambayar bata taso ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel