Gwamna ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisa a jaharsa

Gwamna ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisa a jaharsa

  • Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya yi martani a kan fille kan dan majalisar jaharsa, Hon Okechukwu Okoye, da wasu yan bindiga suka yi
  • Soludo wanda ya nuna kaduwa da takaici kan lamarin, ya saka tukwicin naira miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani kan makasan dan majalisar
  • Ya kuma sha alwashin aiki tare da hukumomin tsaro domin kamowa da hukunta duk wasu miyagu a jaharsa

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya saka tukwicin naira miliyan 10 ga duk mutum ko kungiyar da za ta bayar da bayanai masu amfani da zai kai ga kama makasan dan majalisar dokokin jihar, Hon Okechukwu Okoye.

Idan za a tuna an yi garkuwa da mamba mai wakiltan mazabar Gwamna Chukwuma Soludo, Hon Okechukwu Okoye, a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi

Sai dai kuma, an tsinci kansa a ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, a Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra, ba tare da gangar jikinsa ba.

Gwamna ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisa a jaharsa
Gwamna ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisa a jaharsa Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP
Asali: Getty Images

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren labaran gwamnan, Mista Christian Aburime kuma aka gabatar da ita ga manema labarai a daren Asabar, gwamnan ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisar, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Soludo ya bayyana cewa ya labarin kisan gillar da aka yiwa Hon. Okechukwu Okoye, dan majalisa mai wakiltan mazabar Aguata II a majalisar dokokin jihar cikin kaduwa da tarin bakin ciki.

A cewar gwamnan, an yi garkuwa da Hon Okoye da Cyril Chiegboka a kan hanya a ranar 15 ga watan Mayu.

Ya jajantawa ‘yan uwansa Isuofia, yana mai cewa mai yiwuwa wadannan miyagun da suka kai masa hari tare da kashe ‘yan sanda uku a Isuofia shekaru biyu da suka wuce ne suka kara kaddamar da wannan harin.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Fille Kan Ɗan Majalisar Najeriya Kwanaki Bayan Sace Shi

Soludo ya sha alwashin cewa dole ne a kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika da duk masu aikata laifuka a Anambra tare da hukunta su.

Ya kuma ba mazauna Anambra tabbacin cewa gwamnati ta yanke shawara tare da sabonta jajircewarta tare da hukumomin tsaro na bibiyar miyagu da kuma tabbatar da ganin an hukunta su, rahoton Channels TV.

Majalisar dokokin jihar Anambra ta yi martani kan kisan mamban nata

Hakazalika, majalisar dokokin jihar Anambra ta nuna dimuwa kan labarin kisan gillar da wasu yan bindiga suka yiwa mambanta, Hon Okechukwu Okoye.

A wani jawabi daga kakakin majalisar, Rt Hon Uche Okafor, wanda jami’in hulda da jama’a na majalisar Emma Madu, ya gabatar ga manema labarai, majalisar jihar ta bayyana kisan Okoye a matsayin ‘abun takaici kuma mai karya zuciya’.

Ya bukaci Gwamna Chukwuma Soludo da kada ya yi kasa a gwiwa a kokarinsa na kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Yan majalisar dokokin Yobe sun bayyana gaskiyar lamari kan yunkurin tsige Gwamna Mai Mala Buni gabannin 2023

Dan majalisar ya kuma yi kira ga yan jahar da su hada hannu da gwamnan a wannan hanyar.

Kakakin majalisar yayin da yake mika ta’aziyya ga iyalan marigayi Hon Okoye da ’yan uwansa da Gwamna Soludo da daukacin al’ummar Isuofia a madadin ‘yan majalisar jihar gaba daya, ya roke su da su dauki dangana domin Hon Okoye ya yi rayuwa mai inganci wajen yiwa Allah da jama’a hidima.

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Fille Kan Ɗan Majalisar Najeriya Kwanaki Bayan Sace Shi

A baya mun ji cewa 'Yan bindiga sun halaka dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguta II a Jihar Anambra, Dr Okechukwu Okoye wanda aka fi sani da 'Okey Di Okay', rahoton The Cable.

An sace Okoye ne, dan asalin garin Isuofia, garinsu Chukwuma Soludo, gwamnan Anambra a Aguata a ranar Lahadi 15 ga watan Mayu tare da Cyril Chiegboka, direktan kamfen dinsa.

Da ya ke tabbatar wa The Cable rasuwar, Tochukwu Ikenga, kakakin yan sandan Jihar Anambra, ya ce an tsinci gangan jikin dan majalisar a Nnobi a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka

Asali: Legit.ng

Online view pixel