Yan majalisar dokokin Yobe sun bayyana gaskiyar lamari kan yunkurin tsige Gwamna Mai Mala Buni gabannin 2023

Yan majalisar dokokin Yobe sun bayyana gaskiyar lamari kan yunkurin tsige Gwamna Mai Mala Buni gabannin 2023

  • Mambobin majalisar dokokin jihar Yobe sun yi martani a kan rade-radin cewa suna yunkurin tsige Gwamna Mai Mala Buni
  • Majalisar ta bakin mataimakin shugaban kwamitinta kan harkokin labarai, Abdullahi Bazua, ta bayyana zargin a matsayin kanzon kurege mara tushe
  • Ta kuma bayyana cewa tana da niyar daukar mataki kan kafar yada labaran da ta wallafa rahoton

Yobe - Majalisar dokokin jihar Yobe ta karyata batun yunkurin tsige Gwamna Mai Mala Buni.

Yan majalisar a wani taron tattaunawa da aka yi a Damaturu sun kuma yi barazanar daukar mataki na doka kan mawallafin rahoton, wato NEWS NET GLOBAL kan rahoton da ya bayar, jaridar The Nation ta rahoto.

Mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan kafofin watsa labarai, Abdullahi Bazua ya ce zagin ba komai bane face kanzon kurege, mara tushe da kuma sharri.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu: Majiya ta ce APC ta gama zaban wanda zai gaji Buhari a 2023

Yan majalisar dokokin Yobe sun bayyana gaskiyar lamari kan yunkurin tsige Gwamna Mai Mala Buni gabannin 2023
Yan majalisar dokokin Yobe sun bayyana gaskiyar lamari kan yunkurin tsige Gwamna Mai Mala Buni gabannin 2023 Hoto: Hon Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa majalisar na da cikakken karfin gwiwa kan Gwamna Mai Mala Buni da tsarin shugabancinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Post ta rahoto sanarwar kamar haka:

“Mambobin majalisar na burin watsi da labarin da aka wallafa a wata kafar watsa labarai ta yanar gizo, NEWS NET GLOBAL mai taken “An kammala shirin tsige Gwamna Buni tare da tikitin kai tsaye ga yan majalisa 24 a Yobe”, da kuma bidiyon da wani Mohammed Yakubu Lai-lai ke yadawa a kan haka. Mu dukka mambobin majalisar muna fatan bayyana cewa wannan jawabin karya ne, mara tushe da kuma sharri.
“A halin yanzu mambobin majalisar suna son kara jaddada goyon bayansu da hadin kai ga Maigirma Gwamna Mai Mala Buni saboda mutuntawa da kyakkyawar alakar da ke tsakanin bangarorin gwamnatin biyu.
"Daga karshe, mambobin majalisar na da niyyar daukar matakin shari'a a kan wadanda suka aikata wannan aika aikar."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

An kuma: Dumi a inuwa Ganduje yayin da wani kwamishinansa ya koma NNPP

A wani labarin, mun ji cewa kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arzikin jihar Kano, Shehu Na’Allah Kura, ya yi murabus daga mukaminsa a karkashin mulkin Ganduje.

Rahoton da muka samo daga jaridar Leadership ya ce, daga karshe dai Kura ya koma jam’iyyar NNPP mai tashe a yanzu a jihar ta Kano.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel