Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi

Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi martani a kan rikicin da ya barke a yankin Warji ta jihar kan zagin Annabi da wata mata ta yi
  • Bala Mohammed ya ce gwamnatinsa ta bayar da umurnin fara bincike a kan lamarin tare da daukar alwashin hukunta duk wadanda aka samu da laifi daidai da doka
  • Ya kuma yi kira ga al'umman jihar da su zamo masu hakuri da juna tare da rungumar zaman lafiya

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, ya yi umurnin gudanar da bincike kan rikicin da ya kaure a yankin Katangan da ke karamar hukumar Warji ta jihar kan zargin taba mutuncin Annabi, jaridar Punch ta rahoto.

An tattaro cewa rigima ya fara ne bayan wani wallafa da wata ma’aikaciyar jinya mai shekaru 40, Rhodan Jatau, ta yi wanda ake ganin cin mutunci ne ga addinin musulunci.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Ƴan Sanda Sun Tabbatar An Ƙona Gidaje 6 Da Shaguna 7 a Bauchi

A yayin rikicin da ya kaure, wasu mutane da ba a tabbatar da adadinsu ba ciki harda wani fasto sun jikkata yayin da aka kona gidaje da dama.

Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi
Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Da yake tabbatar da lamarin a ranar Asabar, kakakin yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A ranar 20 ga watan Mayun 2022 da misalin karfe 5:45 na yamma wasu fusatattun matasa sun kona gidaje shida da shaguna bakwai, yayin da wasu mutane suka jikkata sakamakon sakon sabo da wata ma’aikaciyar jinya a karamar hukumar Warji Rhoda Jatau mai shekaru 40 ta wallafa a shafin soshiyal midiya.
“Tuni rundunar yan sanda ta tura tawaga ta musamman, na yan sanda da masu kwantar da tarzoma, wadanda kokarinsu ya daidaita lamarin.
“Zaman lafiya ya dawo yankin a yanzu, yayin da ake gudanar da sintiri don tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wata Mata Ta Sake Zagin Annabi a Bauchi, Matasa Sun Bazama Nemanta, Sun Ƙona Gidaje Sun Raunta Fasto

“Kwamishinan yan sandan ya roki jama’a da su kwantar da hankali da gudanar da harkokinsu ba tare da tsoron razanarwa ba domin zaman lafiya ya dawo yankin da abun ya shafa.”

Daga bisani gwamnan jihar ya ziyarci garin tare da shugabannin hukumomin tsaro da manyan jami’an gwamnati, don duba halin da ake ciki da kuma jajentawa mutanen.

Mohammed ya nuna takaici da bakin cikin faruwar lamarin, yana mai shan alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta nade hannayenta tana kallon wasu marasa kishin kasa suna kawo cikas ga zaman lafiya a jihar ba.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta kafa wani kwamitin bincike domin bankado gaskiyar lamarin kuma duk wanda aka kama da laifi a tsakanin Musulamai da kirista zai fuskanci hukunci daidai da doka.

Mohammed ya ce:

“A gaskiya na ji takaici kuma na yi bakin ciki matuka da faruwar lamarin da ya wakana a Warji saboda Warji gidan zaman lafiya ne. Al’ummar Kirista sun shafe shekaru da yawa suna zaune a Warji. Ko da yake su ne yan tsiraru amma sun zauna lafiya da masu rinjaye. Kuma da na gano cewa wacce ta haddasa wannan tashin hankali da tada zaune tsaye ba ma yar asalin Warji ba ce, sai hankalina ya kwanta da fahimtar hakan.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

“Soshiyal midiya annoba ce, fasaha na da kyau amma wani lokacin, ana iya amfani da shi a kan mu. Ita ma yarinyar da ta fara wannan, ta ari wannan abu ne daga Ghana. Bangaren tsaro ya zo mani da jawabi, amma tabbas, kuskure biyu ba za su iya zama daidai ba. Mu kame kanmu, mu kasance masu zaman lafiya da juna.
“Za mu tabbatar da ganin cewa bamu karfafa wannan ba, dole ne a sanya tukuici da hukunci a kan wannan, kamar yadda Kwamishinan ‘yan sandan ya ce. Amma don Allah, na san da karamin abu, wasu za su biyo baya. An kona gidan wani, dole zai ji ba dadi, don Allah ku yi hakuri da sunan Allah kuma idan ba za ku yi ba saboda ni ko wani abu, ku yi da sunan Allah da ku ka yi imani da shi, domin an san Bauchi da zaman lafiya.
“Kuna ganin ‘yan bindiga a ko’ina, Boko Haram a ko’ina, don Allah ku janye takobi ku, ku rungumi zaman lafiya da juna. Mu duka daya ne.”

Kara karanta wannan

Ana Zaman Ɗar-Ɗar Yayin Da Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai

Gwamnan ya ce ya kasa bacci kan wannan lamarin, yana mai cewa:

“Zuciyata na nan tana ta tunanin matakin da lamarin ya kai amma an gode Allah ba a rasa rai ba.
“Duk wadannan kadarorin daga Allah suke. Za mu kafa bincike don kamo masu laifin sannan za mu kawo dauki ga wadanda suka yi asara. Kada ku sake maimaita wannan abu."

Gwamnatin, a cewar gwamnan, tana yin duk mai yiwuwa domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, kuma ba za ta lamunci duk wani kalubale da zai iya kawo cikas ga jihar ba, rahoton Daily Post.

Matasan Musulmai sun fito neman matar da ta zagi Annabi ruwa a jallo a Bauchi, an harbe mutum 2

A gefe guda, mun kawo cewa jama’a sun shiga tashin hankali a Bauchi kan zargin zagin Annabi da wata ma’aikaciyar kiwon lafiya ta jihar Bauchi, Roda Jatau ta yi, inda ta tura wani bidiyon cin mutuncin Annabi zuwa shafin Whatsapp.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Garo na shirin barin APC duk da zabarsa da aka yi ya gaji Gawuna

An tattaro cewa matasa Musulmai sun bazama neman matar wacce ta kasance yar asalin jihar Gombe amma take aure a yankin Warji da ke jihar, jim kadan bayan sallar Juma’a, amma basu same ta ba saboda an gudun da ita zuwa wani waje.

Hakan ya tunzura fusatattun matasan inda suka lalata kayayyaki mallakar kiristoci a yankin sannan suka cinnawa gidajensu wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel