Buhari ya zalunce ku, idan na zama shugaban ƙasa da ku zan tafi, Tambuwal ga yan kudu maso gabas

Buhari ya zalunce ku, idan na zama shugaban ƙasa da ku zan tafi, Tambuwal ga yan kudu maso gabas

  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ware yankin kudu maso gabas wajen nadin mukamai
  • Tambuwal wanda ke son zama shugaban kasa a 2023, ya ce babu dan kudu maso gabas ko daya a cikin shugabannin manyan hukumomin gwamnati guda 10
  • Sai dai ya bayyana cewa hakan ba zai taba faruwa ba idan har ya zama shugaban kasa, cewa zai yi aiki tare da kowa ba tare da nuna son kai ba

Imo - Gwamnan jihar Sokoto kuma mai neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa zai tafiyar da gwamnati wacce za ta dama da kowa idan aka zabe shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

Da yake magana da mambobin jam’iyyar a Imo a ranar Juma’a, Tambuwal ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ‘ragi’ yankin kudu maso gabas ta hanyar kin nada mutanen yankin a manyan mukaman gwamnati, jaridar The Cable ta rahoto.

Gwamnan ya bayyana cewa mutanen yankin suna ganin an mayar da su saniyar ware a gwamnatin Buhari.

Tambuwal: Buhari ya ragi yankin kudu maso gabas wajen nada mukamai, hakan ba zai faru ba a gwamnatina
Tambuwal: Buhari ya mayar da mutanen kudu maso gabas saniyar ware Hoto: Daily Post
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Post ta nakalto Tambuwal yana cewa:

“Buhari ya ragi yankin kudu maso gabas. Ni ne na shawarci Saraki da ya zabi Ekweremadu domin zama mataimakinsa a 2015. Akwai lamari na mayar da mutanen kudu maso gabas saniyar ware.
“Shugabannin manyan hukumomin gwamnati guda goma ba yan kudu maso gabas bane, ciki harda gwamnan CBN.
“Babu ko daya daga cikin shugabannin tsaro da ya fito daga kudu maso gabas. Shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, mataimakin shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa duk ba yan kudu maso gabas bane. A karkashin kulawata hakan ba zai taba faruwa ba. Za a dama da kowani yanki na kasar nan.”

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Yayin da yake bayyana mutanen kudu maso gabas a matsayin masu kasuwanci, Tambuwal ya ce za a nada su a mukamai masu muhimmanci idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

“Ba za a iya ware yankin kudu maso gabas da musamman jihar Imo ba. PDP za ta kwato Imo idan na zama shugaban kasa. Mutanen Igbo sun san kan kasuwanci. Za ku same ni a matsayin abokin tarayya.
“Muna aiki tare da yan uwanmu a Sokoto. Mun dawo da zaman lafiya yanzu a jihar Sokoto. Zan kasance shugaban kasa ga dukkan yan Najeriya.”

Lalong: Abin Da Yasa Ba Zan Goyi Bayan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ba a APC

A wani labarin, Simon Lalong, ya ce yana goyon bayan Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri kuma dan takarar shugaban kasa na 2023, ya kuma ce ba zai bi bayan wani dan takara daga arewacin Najeriya ba.

The Punch ta ruwaito ta rahoto cewa Lalong ya yi wannan ikirarin ne a Jos, lokacin da Amaechi ya je jihar don jan hankalin wakilan jam’iyyarsu yayin da zaben fidda gwani ya ke kunno kai.

Kara karanta wannan

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

A cewar Lalong, Amaechi ya taka babbar rawa a jiharsa don haka zai samu goyon baya daga duk shugabannin Filato, ciki har da tsohon kakakin majalisar tarayya da ‘yan majalisar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel