Manjo Hamza Al-Mustapha ya yanki tikitin takara kujerar shugaban kasa a 2023

Manjo Hamza Al-Mustapha ya yanki tikitin takara kujerar shugaban kasa a 2023

  • Al-Mustapha zai fito takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya a zaben da zai gudana Febrairun 2023
  • Tsohon Soja kuma Dogarin shugaban kasa ya sayi Fom din takara karkashin jam'iyyar Action Alliance AA
  • Al-Mustapha a baya ya yi takaran kujeran shugaban kasar karkashin jam'iyyar Green Party

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Birnin Abuja - Babban dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya shiga jerin masu neman takara kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Al-Mustapha ya ayyana niyyar takararsa karkashin jam'iyyar Action Alliance AA, rahoton Leadership.

Yayin saya Fam dinsa na takara a hedkwatar jam'iyyar AA dake Abuja ranar Alhamis, jami'in soja mai ritaya ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi yankin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma.

A cewarsa, gwamnatinsa zata samar da cigaba mai dorewa don inganta tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Ka zabi Ganduje matsayin mataimakin shugaban kasa, an yi kira ga Tinubu

Shugaban uwar jamiyyar AA, Cif Kenneth Udeze, ya kalubalanci mambobin jam'iyyar da su yi iyakan kokarinsu wajen ganin cewa yan takaran jam'iyyar sun samu nasara a zabe mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manjo Hamza Al-Mustapha
Manjo Hamza Al-Mustapha ya yanki tikitin takara kujerar shugaban kasa a 2023 Hoto: Al Mustapha
Asali: UGC

Mutum 56 kacal ke hana ruwa tafiya a Najeriya, Manjo Hamza Al-Mustapha

Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewa wasu mutum 56 ke hana ruwa tafiya a Najeriya.

Al-Mustapha yace wadannan mutane 56 ke cinye arzikin Najeriya.

Ya bayyana cewa lokacin da yake daure, yayinda ake azabtar da shi ya fahimci wadannan mutane 56 kuma idan aka samu nasarar kawar da su, Najeriya za ta samu cigaba.

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne yayin hira da sashen Hausa na BBC a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel