Adadin mutanen da ake kashe da wadanda akayi garkuwa dasu a Kaduna cikin watanni 3

Adadin mutanen da ake kashe da wadanda akayi garkuwa dasu a Kaduna cikin watanni 3

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana adadin mutanen da yan bindiga suka sace cikin watanni uku a jihar
  • Yan bindiga sun addabi al'ummar jihar Kaduna musamman baban titin Abuja zuwa Kaduna
  • Gwamnan jihar Kaduna ya bada shawaran tayar da garin Rijana, Katari da Akilubu gaba daya

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana damuwarsa bisa yawaitan yan ta'adan Ansaru da na Boko Haram a jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana cewa hakazalika akwai sabon alaka dake gudana yanzu tsakanin yan bindiga masu garkuwa da mutane da yan Boko Haram.

A cewarsa, wannan alaka ta haifar da harin da aka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga Maris, 2022.

Ya bayyana haka ne a zaman majalisar tsaron jihar na watanni uku-uku da kwamishanan tsaron jihar, Samuel Aruwan, ke gabatar da bayanan tsaro, rahoton TVCng

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Malam El-Rufa'i a jawabinsa ya kara da cewa yanzu yan ta'adda sun fara dasa bama-bamai a jihar.

Saboda haka yana kira ga gwamnatin tarayya ta kafa tiyata na Sojoji a jihar kamar yadda aka yi a Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samuel Aurwan
Adadin mutanen da ake kashe da wadanda akayi garkuwa dasu a Kaduna cikin watanni 3 Hoto:KDSG
Asali: UGC

Shi kuma Kwamishanan tsaron, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa akalla mutum 360 aka kashe sakamakon hare-haren yan bindiga kuma an yi garkuwa da mutane 1,389 tsakanin watar Junairu da Maris na shekarar nan.

A cewarsa, mazabar tsakiyar Kaduna wannan kashe-kashe da hare-hare suka fi aukuwa.

Yan bindiga sun sako matar da ta shiga daji taimakawa Fulani, sun rike diyarta da direba

Malama a kwalejin fasahar KadPoly wacce yan bindiga suka sace lokacin da ta shiga daji rabawa Fulani kayan azumi, Dr Rahmatu Abarshi, ta samu kubuta.

A watan Afrilu, yan bindiga sun saceta tare da diyarta da direbanta.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Shugaban kamfanin Liberty TV da safiyar Alhamis ya tabbatar da labarin cewa an sako ta.

A cewarsa:

"An sak Lakcarar amma diyarta, Ameerah da direbanta har yanzu na hannun yan bindigan"

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng