Katsina: Ƴan sanda sun sheƙe 'yan bindiga 6, sun kwace makamai da dabbobin sata

Katsina: Ƴan sanda sun sheƙe 'yan bindiga 6, sun kwace makamai da dabbobin sata

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun dakile harin'yan ta'addan da suka kai farmaki kauyen Dabaibayawa na Batagarawa da kauyen Dankiri na karamar hukumar Dutsinma
  • 'Yan sandan basu tsaya nan ba, sai da suka sheke wasu daga cikin 'yan ta'addan bayan wadanda suka tsere da miyagun raunuka
  • Tawagar 'yan sandan ta sheke shida daga cikin 'yan ta'addan, sannan ta kwace bindiga kirar AK-47, da shanu 110 da raguna da akuyoyi 242 a lokuta daban-daban

Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce ta dakile harin 'yan bindiga a kauyen Dabaibayawa na Batagarawa da kauyen Dankiri na karamar hukumar Dutsinma.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Katsina akan ayyukansu na cikin kwanakin nan a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Bayan mance batun takara, ministocin Buhari 2 sun hallara a taron FEC

Katsina: Ƴan sanda sun sheƙe 'yan bindiga 6, sun kwace makamai da dabbobin sata
Katsina: Ƴan sanda sun sheƙe 'yan bindiga 6, sun kwace makamai da dabbobin sata. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

SP Isah ya bayyana yadda rundunar ta sheke wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne, tare da gano bindiga kirar AK-47, shanu 110 da raguna da akuyoyi 242.

"A ranar 17 ga watan Maris, 2022, rundunar ta samu kiran gaggawa a kan cewa 'yan bindiga sun auka kauyen Dantakiri na karamar hukumar Dutsinma, inda suka sace dabbobin gida da ba a san adadi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kwamandan yankin na tawagar 'yan sandan Dutsinma da 'yan sa kai sun tare 'yan ta'addan a Mararrabar-Sayaya ta karamar hukumar Matazu.
"Tawagar tayi musayar wuta da hatsabiban, inda ta sheke shida daga cikin 'yan ta'addan, sannan ta gano shanu 86 da raguna da akuyoyi 101," cewarsa kamar yadda The Nation ta rahoto.
"Yayin bincikar wurin da lamarin ya auku, an gano bindiga kirar AK-47 guda daya. Hakan na nuna cewa wasu daga cikin 'yan ta'addan sun ranta a na kare da raunukan harsasai.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun kashe 3 a dangin shugaban karamar hukuma da mai gadi

"Tawagar bincike na cigaba da bincikar dajikan kusa da sa ran damko 'yan ta'addan da suka samu raunuka ko gano gawawwakinsu da makamansu," a cewarsa.

Isah ya kara da bayyana yadda a wannan ranar, suka samu kiran gaggawa a kan yadda 'yan ta'adda masu yawa, tare da bindigu kirar AK-47, suka kai farmaki gonar AIG mai ritaya, Lawal Mani, a kauyen Dabaibayawa, inda suka yi awon gaba da dukkan dabbobin gidan dake wurin.

A cewarsa, "An sanar wa OC sashin yaki da garkuwa da mutane, DPO na Batagarawa da na Batsari don su wartaka gami da tarar hatsabiban yayin da suke kokarin shiga dajin Rugu a dabbobin da suka sace.
"Daga bisani, tawagar ta yi nasarar tare da dakilesu a kauyen Kandawa na karamar hukumar Batsari.
"Tawagar tayi musayar wuta da 'yan ta'addan, inda ba wai nasarar dakile harinsu kadai tayi ba, sai da ta gano dabbobin da suka sace wadanda suka hada da; shanu 24 da raguna da akuyoyi 141. Sannan ana cigaba da bincike."

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

Kakakin 'yan sandan ya kara da bayyana yadda rundunar tayi nasarar gano mota cike da barayi, gami da gano wasu motoci da aka sace.

Haka zalika, ya bayyana yadda suka damko wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne, sannan sun amsa cewa sun kai hari da dama a kauyukan dake karamar hukumar Safana na jihar.

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai sabon farmaki, sun halaka mutum 7

A wani labari naa daban, 'yan bindiga sun kai hari wani yankin Zamfara, gami da halaka mutane bakwai a ranar Asabar, wata majiya a Maradun ta bayyana yadda aka hari kauyuka biyu, Faru da Kauyen Minane.

"Sojoji sun kai gawawwakin wadanda aka halaka babban asibitin Maradun," a cewar Jamilu Muhammad.
"Mutanenmu dake kauyen Minane sun bayyana yadda 'yan bindiga suka auka musu misalin karfe 2:00 na rana, gami da bude musu wuta. Abunda suka saba shi ne bincika gida-gida don neman dabbobin gida da sauran mahimman abubuwa amma jiya, a lokacin da suka auko harbe-harbe suka yi tayi babu kakkautawa," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng