Zamfara: 'Yan bindiga sun kai sabon farmaki, sun halaka mutum 7

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai sabon farmaki, sun halaka mutum 7

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun fada kauyukan Faru da Minane a jihar Zamfara inda suka halaka rayuka bakwai
  • An gano cewa, sun shiga kauyukan karamar hukumar Maradun din da rana wurin karfe biyu inda suka dinga harbe-harbe
  • Majiya ta tabbatar da cewa sojoji sun mika wadanda suka rasa rayukansu zuwa babban asibitin Maradun

Zamfara - 'Yan bindiga sun kai hari wani yankin Zamfara, gami da halaka mutane bakwai a ranar Asabar, wata majiya a Maradun ta bayyana yadda aka hari kauyuka biyu, Faru da Kauyen Minane.

"Sojoji sun kai gawawwakin wadanda aka halaka babban asibitin Maradun," a cewar Jamilu Muhammad.
Zamfara: 'Yan bindiga sun kai sabon farmaki, sun halaka mutum 7
Zamfara: 'Yan bindiga sun kai sabon farmaki, sun halaka mutum 7. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Mutanenmu dake kauyen Minane sun bayyana yadda 'yan bindiga suka auka musu misalin karfe 2:00 na rana, gami da bude musu wuta. Abunda suka saba shi ne bincika gida-gida don neman dabbobin gida da sauran mahimman abubuwa amma jiya, a lokacin da suka auko harbe-harbe suka yi tayi babu kakkautawa," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

A cewarsa, an halaka mutane shida a kauyen Minane, yayin da aka halaka daya a kauyen Faru. Ya ce, akwai yuwuwar karuwar yawan wadanda suka rasa rayukansu saboda har yanzu ba a san inda wasu suke ba a kauyukan da lamarin ya auku, Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An birne wadanda suka rasa rayukansu a Maradun saboda komawa jana'iza kauyukan ba zai yuwu ba, saboda tsoron dawowar 'yan bindigan" majiyar tace.

Channels TV ta rahoto cewa, sai dai, kakakin 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu, bai amsa kiraye-kirayen waya da sakonnin da aka tura masa ba.

JTF sun halaka 'yan bindiga 10 a Niger bayan sun yi yunkurin hargitsa shagalin sallah

A wani labari na daban, jami'an tsaro sun sheke a kalla 'yan bindiga guda goma yayin da suka yi yunkurin tarwatsa shagalin bikin sallar azumi a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Kwamishinan kananan hukumomi, Emmanuel Umar ne ya tabbatar da aukuwar lamarin jiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya ce, 'yan bindiga sun kai hari kauyen Kawo da Uregi a ranar Litinin ana tsaka da shagalin bikin karamar sallah.

A cewarsa, jami'an tsaron hadin guiwa ne suka ceto wadanda aka yi garkuwan dasu guda 14, tare da kwace babura bakwai na miyagun 'yan ta'addan.

The Cable ta ruwaito cewa, jami'an tsaron sun yi hanzarin dakile harin, gami da isa wurin da hatsabiban ke cin karensu babu babbaka a wuraren Uregi da kauyukan Kiribo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel