Daga karshe: Bayan mance batun takara, ministocin Buhari 2 sun hallara a taron FEC

Daga karshe: Bayan mance batun takara, ministocin Buhari 2 sun hallara a taron FEC

  • Bayan janyewa daga takara, ministocin Buhari sun bayyana a harabar taron FEC na yau Laraba 18 ga watan Mayu
  • Wannan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da suka bayyana ficewarsu daga takara bayan da Buhari ya basu zabi
  • A baya shugaba Buhari ya ce duk ministan da ke son tsayawa takara dole ya bar kujerarsa ya koma takara gadan-gadan

Abuja - Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Ministan Harkokin Mata, Pauline Tallen sun halarci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na wannan makon a fadar Shugaban kasa, Abuja bayan ganawarsu da Buhari kan batun yin murabus a makon jiya.

Ministocin tare da wasu mutane takwas da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takara a ofisoshi daban-daban a zaben 2023, shugaban ya bukaci su yi murabus nan take a makon da ya gabata, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan a Abuja

Bayan janye takara, ministocin Buhari sun halarci FEC
Da dumi-dumi: Ministocin Buhari 2 sun hallara a taron FEC bayan fita daga tseren takara | Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Sai dai kuma hudu daga cikin Ministocin da suka hada da na Kwadago da Aiki, Dokta Chris Ngige; Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva; Malami da Tallen, sun fasa tsayawa takara, sun zabi ci gaba da zama a mukamansu.

Yayin da Malami ke neman kujerar gwamnan jihar sa ta Kebbi, Tallen ta yi yunkurin shiga tseren tikitin takarar sanatan Filato ta Kudu da Gwamna Simon Lalong da sauran su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ngige da Sylva kuwa sun tsaya takarar shugaban kasa, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Ngige dai bai halarci taron ba, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kafin a fara taron majalisar zartaswar da shugaba Buhari ya jagoranta, an yi shiru na minti daya don karrama tsohon ministan sadarwa na gwamnatin Janar Ibrahim Babangida, Olawole Adeniji Ige, wanda ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Tsohon Shugaban APC, Oshiomhole ya fallasa Gwamnan da ya roke shi ya murde zabe a 2020

A wani labarin, mai girma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya karyata Adams Oshiomhole a kan zargin da ya jefe shi da shi na neman ya murde zabe.

Gwamna Kayode Fayemi ya musanya wannan zargi da Adams Oshiomhole ya yi a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin Channels a makon nan.

A hirar da aka yi da Oshiomhole, ya bada labarin yadda gwamnan na Ekiti ya bukaci ya yi amfani da karfinsa domin ya yi son kai a wajen bada takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel