Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

  • Wata sanarwa ta bayyana adadin mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tulun iskar gas a jihar Kano
  • A yau ne aka samu aukuwar wata fashewa da ta kai ga tada hankalin al'umma a wani yankin jihar Kano
  • Jami'an tsaro sun bayyana yadda lamarin ya faru, inda suka ce tulun gas ne ya fashe ba wai tashin nakiya ba

Jihar Kano - Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar tulun iskar gas da ta afku a jihar Kano a ranar Talata ya karu zuwa tara.

Ma’aikatar Agajin Gaggawa ta Tarayya ce ta bayyana haka a lokacin da take sanar da isowar babban daraktan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, Mustapha Habib Ahmed, a inda lamarin ya faru, rahoton Punch.

fashewar wani abu a Kano
Fashewar wani abu a Kano: Adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 9 | Hoto: bbc.com
Asali: Twitter

Tun da farko dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane hudu, inda ta ce tulun iskar gas ne ya fashe ba bam ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun aike da sakon sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

A cewar ma'aikatar ta Twitter:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 9 daga baraguzan ginin da ya ruguje a gefen wata makarantar firamare sakamakon fashewar wani tulin iskar gas a hanyar Aba dake unguwar Sabon Gari a jihar Kano.
“DG @nemanigeria Mustapha Habib Ahmed yana wurin da lamarin ya faru kuma yana lura aikin ceton. A halin yanzu NEMA tana gudanar da ayyukan ceto tare da hukumomi ‘yan uwanta.”

Tsagerun 'yan bindiga sun kirgo kananan hukumomi 9 da za su addaba a Anambra

A wani labarin na daban kun ji cewa, wasu da ake zaton yan bindiga ne sun lissafa kananan hukumomi tara a jihar Anambra wanda za su kaiwa hari kwanan nan, jaridar The Nation ta rahoto.

Ci gaban na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun kashe mutane hudu da ke tabbatar da dokar zaman gida a ranar Talata a Ogidi, karamar hukumar Idemili North.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Fashewar Tulun Gas, Ta Ce Ba a Makaranta Abin Ya Faru Ba

Kananan hukumomin da aka lissafa don kaiwa harin sune: Ihiala, Aguata, Nnewi South, Awka North, Awka South, Idemili North, Idemili South, Orumba South, Orumba North da Anambra East.

Asali: Legit.ng

Online view pixel