APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

  • Adamu Garba II, dan takarar shugaban kasa a 2023 ya sayi fom din tsayawa takara da kuma nuna sha'awarsa ta gaje Buhari
  • Garba wanda ke neman kujera ta daya a Najeriya ya ce yana shirin fitar da 'yan kasar ne daga kangin talauci da wasu kalubale da dama da suke fuskanta
  • A cewar dan takarar shugaban kasan a 2023, manyan jam’iyyun siyasa biyu a Najeriya ba su da wani shiri ga ci gaban matasa

Abuja - Wani mai fatan zama shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 mai zuwa, Adamu Garba, ya sayi fom din tsayawa takara bayan dogon cece-kuce, rahoton TheCable.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a Abuja a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, bayan siyan fom din, dan takarar na YPP na neman kujerar shugaban kasa ne domin gyara wasu daga cikin matsalolin da ‘yan kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya

Adamu Garba ya sayi fom a jam'iyyar YPP
APC da PDP ba na mata bane: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP | Hoto: @adamugarba
Asali: Twitter

Garba wanda ya karbi fom din sa a sakateriyar jam’iyyar YPP ta kasa ya ce ya sayi takardun biyu ne domin kawar da fatara, hauhawar farashin kayayyaki, yawan mace-macen mata da kananan yara da rashin ilimi da dai sauransu daga doron Najeriya.

Legit.ng ta tattaro cewa fom din takarar shugaban kasa da nuna sha'awar jam'iyyar YPP ya kai Naira miliyan 15 amma Garba ya sayi nasa ne a kan Naira miliyan 7.5 sakamakon rangwamen 50% bisa 100% idan aka yi la'akari da shekarunsa (38).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar YPP ta rage kudin fom da 50% ga 'yan jam'iyyar da ba su kai shekaru 40 ba.

Garba zai fafata ne da Malik Ado-Ibrahim, wani mai fatan takarar shugabancin kasa a 2023 na jam'iyyar YPP.

A ci gaba da neman takarar shugaban kasa, Adamu ya yi kira ga matasan Najeriya a fadin kasar da kuma kasashen ketare da su yi watsi da jam'iyyun PDP da APC.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai yi ritaya daga siyasa ba har sai ya zama shugaban Najeriya.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zayyana neman kuri’un wakilan jam’iyyar a Makurdi, babban birnin jihar Benue a ranar Talata, rahoton Daily Trust.

A cewarsa:

“Matasan Benue ku dage don ganin an gyara muku katunan zabe. Ina tare da ku, sauran takwarorina a nan suna tare da ku da kuma sauran da dama da ba sa nan suna tare da ku don tabbatarwa da da fatan samun dunkulewar Najeriya mai albarka gare ku."

Asali: Legit.ng

Online view pixel