Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun kashe 3 a dangin shugaban karamar hukuma da mai gadi

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun kashe 3 a dangin shugaban karamar hukuma da mai gadi

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki gidan shugaban karamar hukuma, sun aikata mummunan barna
  • An ruwaito cewa, sun hallaka dangin shugaban har uku tare da kashe mai gadin da ke bakin aikinsa a gidan
  • Ya zuwa yanzu dai hukumar 'yan sandan jihar bata ce komai kan lamarin ba, amma dai majiya ta tabbatar

Jihar Ebonyi - Wasu ‘yan bindiga sun kashe dangin shugaban karamar hukumar Ikwo ta jihar Ebonyi, Steve Orogwu, su uku.

Wata majiya ta shaida wa jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan shugaban ne da ke Ekpaomaka a daren ranar Talata amma ba su same shi a gida ba.

Maharan sun harbe danginsa uku da kuma mai gadin da ke bakin aiki a gidan har lahira.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Yadda 'yan bindiga suka kashe dangin shugaban karamar hukuma
Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun kashe 3 a dangin shugaban karamar hukuma da mai gadi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Orogwu ya tabbatar wa wakilin jaridar faruwar lamarin cikin wata murya mai cike da rudewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Sun kai hari gidana da daddare suka kashe babban yayana da 'ya'yansa biyu da kuma mai gadinmu".

Ya kuma ce ‘yan bindigar sun bankawa gidan dangin nasa wuta.

An kuma bayyana cewa an kai gawarwakin wadanda aka kashe zuwa dakin ajiye gawa a Abakaliki.

Ba a iya gano dalilin kai harin ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, kafar labaran Tori ta tattaro.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Ebonyi Loveth Odah ta ce ba ta je wurin aiki ba lokacin da aka tuntube ta domin jin ta bakinta.

Tserewa zai yi: Yadda aka kaya a kotu kan batun belin shugaban 'yan IPOB Nnamdi Kanu

A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Laraba, ta ki bayar da belin shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, har sai an yanke hukunci kan laifin cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ta maka shi a kotu a kai.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan a Abuja

Mai shari’a Binta Nyako ta ce dole ne Kanu ya bayyana dalilin da ya sa ya ci zarafin belin da aka ba shi a baya, kafin ya samu wani sassaucin beli daga kotun, Vanguard ta ruwaito.

A cewar mai shari'a Nyako:

“Har sai an tabbatar da batun rashin halartar wanda ake kara domin shari’ar da ake yi masa, tare da duk sharuddan belin da aka saba, bukatar belin a nan take zai zama ya yi sauri, don haka kotu ta hana belin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel