Da duminsa: Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan a Abuja

Da duminsa: Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan a Abuja

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, sun shiga labule a ranar Talata, 17 ga watan Mayu
  • Jiga-jigan na jam'iyyar PDP sun gana ne a gidan tsohon shugaban kasar da ke babbar birnin tarayya Abuja
  • Ana sanya ran za su tattauna kan batutuwan da suka shafi jam'iyyar adawar da kuma makomar Najeriya gabannin zaben 2023

Abuja - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yi ganawar sirri tare da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a ranar Talata, 17 ga watan Mayu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa shugabannin sun saka labulen ne a gidan tsohon shugaban kasar da ke babbar birnin tarayya Abuja.

Ortom ya rike mukamin karamin ministan kasuwanci, sannan daga bisani ya zama ministan sa ido a ma’aikatar sufurin jiragen sama a karkashin gwamnatin Jonathan.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Da duminsa: Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan a Abuja
Da duminsa: Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan a Abuja Hoto: Newsdirect
Asali: UGC

An tattaro cewa za su tattauna batutuwan da suka shafi PDP da nasararta gabannin zaben 2023 mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da aka tuntube shi, sakataren labaran Ortom, Nathaniel Ikyur, ya ce:

“Shugabannin biyu sun gana a cikin sirri tsawon sama da mintuna 40 sannan sun tattauna gaskiya.
“Koda dai babu wani daga cikinsu da ya zanta da manema labarai a lokacin da suka fito, sun kasance dauke da murmushi a fuskokinsu inda tsohon shugaban kasar ya gaisa da kowa a tawagar gwamnan.”

Ya ci gaba da cewa:

“Shakka babu sun tattauna lamuran jam’iyyar Peoples Democratic Party da makomar Najeriya.”

Wasu daga cikin hadiman gwamnan da suka raka shi sun hada da Dr James Anbua, babban mataimaki na musamman; Hon Steven Amase, babban sakatare mai zaman kansa na gwamna, da Hon Abrahams Kwaghngu, babban mataimaki na musamman kan ayyuka na musamman.

Kara karanta wannan

Al’ummar gari sun tsere cikin jeji yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

Shirin 2023: Tsoffin gwamnonin Jigawa sun gama kai a PDP, domin kassara APC a jihar

A wani labarin, mun ji cewa a ranar Litinin ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki, ya koma jam’iyyar PDP inda ya kawo karshen zamansa a jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan.

Turaki ya koma PDP ne tare da jiga-jigan ‘yan siyasa na jam’iyyar APC na gundumarsa ciki har da tsohuwar kwamishiniyar harkokin mata a jihar, Ladi Dansure.

Tsohon gwamnan ya shaidawa manema labarai a gidansa na Kano cewa ya koma jam’iyyar PDP ne domin ciyar da jihar Jigawa gaba da kuma ‘yantar da jama’a daga mulkin kama-karya na 'yan APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel