Tserewa zai yi: Yadda aka kaya a kotu kan batun belin shugaban 'yan IPOB Nnamdi Kanu

Tserewa zai yi: Yadda aka kaya a kotu kan batun belin shugaban 'yan IPOB Nnamdi Kanu

  • Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta ki ba da belin Nnamdi Kanu duba da wasu batutuwan da suka shafi tsaro
  • Bangaren gwamnati ta roki a hana belin Kanu saboda yiwuwar ya tsere ganin girman lafin da ake tuhumarsa dashi
  • Hakazalika, kotun ta ce Nnamdi Kanu zai iya sake shigar da batun belin, amma kotu za ta so gaggauta yin shari'ar ba batun beli ba

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Laraba, ta ki bayar da belin shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, har sai an yanke hukunci kan laifin cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ta maka shi a kotu a kai.

Mai shari’a Binta Nyako ta ce dole ne Kanu ya bayyana dalilin da ya sa ya ci zarafin belin da aka ba shi a baya, kafin ya samu wani sassaucin beli daga kotun, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Fashewar Tulun Gas, Ta Ce Ba a Makaranta Abin Ya Faru Ba

An hana belin Kanu a kotu
Da dumi-dumi: Kotu ta ki amincewa da ba da belin shugaban 'yan IPOB Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

A cewar mai shari'a Nyako:

“Har sai an tabbatar da batun rashin halartar wanda ake kara domin shari’ar da ake yi masa, tare da duk sharuddan belin da aka saba, bukatar belin a nan take zai zama ya yi sauri, don haka kotu ta hana belin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Duk da haka, wanda ake tuhuma yana da 'yancin sake shigar da bukatar belin."

Inda baraka ta fara a shari'ar Nnamdi Kanu

Kotun ta yi nuni da cewa, shari’ar Kanu ta samu koma baya ne tun a 2015, sakamakon wasu kararraki 19 da aka shigar a kan batun, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Don haka, ta roki bangarorin da su ba da damar a ci gaba da shari’ar don a iya tantance laifin, ko sabanin haka.

A bukatar belin da ya shigar, Kanu, ya shaidawa kotun cewa an gana masa azaba mai tsanani na tsawon kwanaki takwas a kasar Kenya, kafin daga bisani a kawo shi gida Najeriya domin ci gaba da shari'arsa.

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Ya yi zargin cewa yanayin lafiyarsa ya tabarbare, biyo bayan “wani abu mai guba” da ya ce an yi masa allurarsa, wanda ya ce yana sa shi ciwon ciki da kuma bugun zuciya.

Da yake nanata cewa hukumar ta DSS ba ta da wuraren da suka dace da duba lafiyarsa, Kanu ya shaida wa kotun cewa an tsare shi ne shi kadai inda ya yi zargin cewa a kullum yana gab da shiga tabin hankali.

Shugaban na IPOB ya shaida wa kotun cewa yana da “amintattun tsayayya”, da suka yi alkawarin cewa ba zai aikata wani laifi ba yayin da yake kan beli.

Baya ga haka, Kanu, ya ce babu wata kotun kasar da ta yi masa shari’a ko kuma ta yanke masa hukunci, yana mai cewa yana da damar a bayar da belinsa.

Ya kuma ja hankalin kotun cewa a baya an sake shi ne bisa dalilin rashin lafiya.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Sai dai gwamnati, ta bukaci kotun da ta ki amincewa da neman belin, inda ta dage cewa Kanu, da ya fahimci girman karar, zai gudu ne daga kasar, kuma ba zai mika kansa gaban kotu ba.

FG Ta Yi Garambawul a Tuhumar Nnamdi Kanu, Ta Lissafa Lauyoyinsa Cikin Wadanda Ake Tuhuma

A wani labarin, Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta sake gurfanar da tsararren shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, kan sabbin tuhume-tuhume shida masu alaka da cin amanar kasa, rahoton Vanguard.

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Mai Shari'a Binta Nyako ta tsayar da rana domin sauraron bukatar da Kanu ya shigar na neman a bada shi beli.

Wani cikin tawagar lauyoyin Kanu, wanda ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa a ranar Laraba, FG ta yi kwaskwarima a tuhume-tuhumen da ta ke yi wa Kanu, inda ta lissafa lauyoyinsa Ifeanyi Ejiofor da Maxwell Opara, a matsayin wadanda ake tuhuma, The Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Sauya Ra'ayinsa Kan Tikitin APC, Ya Nuna Alamun Zai Amince Ya Yi Takarar

Asali: Legit.ng

Online view pixel