Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Fashewar Tulun Gas, Ta Ce Ba a Makaranta Abin Ya Faru Ba

Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Fashewar Tulun Gas, Ta Ce Ba a Makaranta Abin Ya Faru Ba

  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce yi karin haske game da fashewar tulun gas a unguwar Sabon Gari, karamar hukumar Fagge
  • Kwamishinan Labarai na Kano, Muhammad Garba, ya ce ba a makaranta bane tulun gas din ya fashe, a wani wurin ajiyar abincin dabobi ne da ke kallon makarantar
  • Garba ya yi kira ga al'umma su kwantar da hankulansu domin gwamnati ta fara bincike a kan lamarin kuma za ta sanar da al'umma abin da ake ciki nan gaba

Gwamnatin Jihar Kano, a ranar Talata ta ce ba a makaranta ne fashewar tulun gas ya faru a Sabon Garin Kano ba, The Nation ta rahoto.

Kwamishinan Labarai, Malam Muhammad Garba, wanda ya yi karin hasken ya ce fashewar ya faru ne a wani wurin ajiye abincin dabobbi 'da ke kallon makarantar' a Aba Road, Sabon Gari, karamar hukumar Fagge.

Kara karanta wannan

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

Ba A Makaranta 'Tulun Gas' Ɗin Ya Fashe Ba, Gwamnatin Kano Ta Yi Ƙarin Haske
Gwamnatin Jihar Kano Ta Ce Ba a Makaranta 'Tulun Gas' Ya Fashe Ba. Hoto: The Nation.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Nation ta tattaro cewa wasu na fargabar cewa yan ta'adda sun fara kai hari makarantu a Kano bayan abin da ya faru a kusa da makarantar Winners Kid Academy.

Amma Garba ya ce:

"Kawo yanzu ba a tantance dalilin fashewar abin da kuma barnar da ya yi ba a hukumance, tuni an fara bincike kuma za a dauki matakai.
"Muna kira ga mutanen jihar, musamman wadanda ke zaune a unguwar, su kwantar da hankulansu yayin da gwamnati da hukumomin da abin ya shafa ke aiki kan lamarin."

Kwamishinan ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta cigaba da yi wa al'umma bayani kan cigaban da ake samu ya kuma gargadi mutane su guji yada labaran da ba a tabbatar ba.

Wata mazauniyar Sabon Gari ita ma ta tabbatar ba a makaranta bam din ya tashi ba

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Legit.ng ta samu ji ta bakin wata budurwa wacce ta ce shagonsu na kusa da wurin da tulun gas din ya fashe, tana mai cewa ta yi mamakin yadda fashewar ya yi wa ginin makarantar illa.

Budurwar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce cikin wadanda suka mutu akwai wani mai sana'ar walda domin har sasan jikinsa ya fado kusa da shagonsu.

"Akwai wani mai walda da ke da shago cikin wadanda suka rasu. Karfin fashwar gas din ya yi dai-dai da sassan jikinsa, kafarsa ta ta yi tsalle ta fado a gaban shagon mu a Aba Road.
"Abin ya faru ne a layin mu, shagon mu yana gini na biyar daga inda abin ya faru," a cewar ta.

Ta kara da cewa daga bisani jami'an tsaro sun iso wurin sun bukaci mutane su bada sarari domin jami'ai su yi aikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel