Yayin da zaben 2023 ya karaso, EFCC ta shiga binciken kudin PDP da APC a bankuna

Yayin da zaben 2023 ya karaso, EFCC ta shiga binciken kudin PDP da APC a bankuna

  • Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya ta na bincike a kan jam’iyyun PDP da APC
  • Ana tuhumar APC mai mulki da PDP mai hamayya a kan zargin wawurar kudi ta wasu bankuna
  • Wani jami’in EFCC ya aika takardu zuwa ga bankuna biyu, ya sanar da su game da binciken da ake yi

Abuja - Premium Times ta fitar da wani rahoto na musamman da ya bayyana cewa hukumar ta na binciken wasu kudi da suka shiga asusun PDP da APC

Shugaban sashen gudanarwa na hukumar EFCC ta kasa, Michael Wetkas ya aika takarda zuwa ga shugabannin wasu manyan bankuna biyu da su ke Abuja.

Wadannan wasiku sun shigo hannun jaridar, inda aka fahimci jami’in hukumar ya sanar da bankunan cewa ana binciken kudin da suka shigo masu.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

EFCC ta sanar da bankunan cewa akwai wasu akawun 14 da ake bincike a kansu. Akawun din na jam’iyyun siyasar ne da wani kamfani mai alaka da PDP.

Ana binciken wasu akawun

Kamar yadda rahoton ya bayyan akawun uku da aka samu daga daya daga cikin bankunan na jam’iyyar APC ne; 0692988080, 0035644896 sai 0044183689.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai wani akawun mai lamba 0054586830, wanda sakatariyar jam’iyyar PDP ta mallaka.

Buhari da mayan EFCC
Buhari ya kawo dokokin da za su karfafi EFCC Hoto: @officialefcc
Asali: Facebook

Wetkas a wasikar da ya aika, ya bayyana cewa ana binciken wasu asusu da APC ta bude a wani fitaccen banki; 0692988080, 0035644896 da kuma 0044183689.

Ana kuma bin diddikin kudin da suka shiga cikin wani akawun na APC da asusu shida da PDP ta bude domin tara kudin kamfe da na kula da sha’anin jam’iyya.

Kamar yadda doka ta bada dama, EFCC za ta bukaci a aiko mata takardar bude akawun din da bayanin kudin da suka shiga ko suka fita a cikin shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Dubunnan ‘Ya ‘yan APC sun yi watsi da Jam’iyya mai mulki zuwa NNPP a jihar Zamfara

Kudin saida fam

Zuwa yanzu ba a tabbatar ko binciken yana da alaka da zaben 2023 da ake shirin yi ba. A halin yanzu jam’iyyu su na samun kudi sosai ta hanyar saida fam.

Kafin ‘dan siyasa ya iya shiga takara a jam’iyya, dole ne sai ya yanki fam a kan farashi mai tsada.

A dalilin haka ne manyan jam’iyyun siyasa da ake da su, suka tara biliyoyin kudi musamman daga hannun wadanda suka fito neman takarar shugaban kasa.

Ana karya da sunan takara

A makon nan aka samu labari cewa, Ken Nnamani ya ce a cikin masu biyan N100m, su saye fam, akwai wanda da kyar su ke iya biyan hayar gidan da suke zama.

Sanata Nnamani ya yi kaca-kaca da kungiyoyin karyan da ke karambanin sayawa ‘yan siyasa fam, ya ce duk mai niyyar darewa kujerar siyasa, ya saye fam dinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel