Dubunnan ‘Ya ‘yan APC sun yi watsi da Jam’iyya mai mulki zuwa NNPP a jihar Zamfara

Dubunnan ‘Ya ‘yan APC sun yi watsi da Jam’iyya mai mulki zuwa NNPP a jihar Zamfara

  • ‘Yan siyasa su na ta lissafi da sauya-sheka daga wannan gida zuwa wannan gida gabanin zaben 2023
  • A irin haka jam’iyyar APC mai mulki ta rasa tsofaffin Kansilolin da aka yi a Zamfara zuwa NNPP
  • Ana maganar dubunnan mutane ne suka fice daga APC, su ka shiga jam’iyya mai kayan marmari

Zamfara - Daruruwa zuwa dubunnan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne suka sauya-sheka a jihar Zamfara, suka rungumi NNPP mai hamayya.

Kamar yadda aka rahoto a gidan talabijin na TVC a ranar Laraba, NNPP ta karu da wata kungiya ta tsofaffin kansiloli da aka taba yi a jihar Zamfara.

Shugaban wadannan tsofaffin kansiloli ne ya jagoranci sauran ‘yan siyasan da suka fusata da irin kamun ludayin APC, aka yi masa wanka a NNPP.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

Rahoton ya bayyana cewa kungiyar ta na ikirarin tana da mutane fiye da 10, 000 a karkashinta.

Shugaban wannan gayya ya ce sun ga abubuwa dabam-dabam da kalubale iri-iri da ya kamata gwamnatin APC mai-ci ta gyara, amma ba tayi ba.

Ganin yadda ake tafiya ta sa shi da dubunnan ‘yan kungiyarsa suka hakura da zama a APC.

Dubunnan ‘yan Kwankwasiyya
Magoya bayan Kwankwasiyya/NNPP a Kano Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

NNPP ta na kara karfi a Najeriya

Kamar yadda wani jigo a NNPP kuma jagoran tafiyar darikar Kwankwasiyya a jihar Zamfara, ya bayyana, NNPP na kara karfi, ta na jan hankalin jama’a.

‘Dan siyasar ya shaidawa manema labarai a zantawar da aka yi da su cewa, jam’iyyar adawar ta NNPP ta na sa ran kai labari a zabe mai zuwa na 2023.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Shugabannin jam’iyya na jihar Zamfara sun karbe tsofaffin ‘ya ‘yan na APC, su ka kuma yi masu bayanin manufofin tafiyar wannan jam’iyyar da suka bi.

Dole a kawo sauyi - Shugaban NNPP

Mohammed Sani wanda shi ne shugaban jam’iyyar NNPP na reshen jihar Zamfara, ya bayyana cewa ba zai yiwu a cigaba da tafiya a yadda ake a yau ba.

Alhaji Sani ya zargi gwamnatin APC da yaudarar jama'a, a maimakon sama masu mafita. Shugaban jam’iyyar ya yi alkawari za su kawo sauyi a kasa.

NNPP ta na yi wa APC ta'adi a Kano

A makon nan aka ji labari guguwar NNPP na neman ratsa siyasar Kano, domin alamu sun tabbata Ibrahim Shekarau da Kawu Sumaila za su fice daga APC.

Ana tunanin sauran wadanda za su shiga NNPP sun hada da Haruna Dederi da Nasiru Auduwa. Hakan na zuwa ne bayan APC ta rasa Tijjani Jobe da Kabiru Rurum.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Asali: Legit.ng

Online view pixel