Yajin aiki: Malaman jami'a sun fusata, sun dauki mataki kan Buhari bisa hana su albashi

Yajin aiki: Malaman jami'a sun fusata, sun dauki mataki kan Buhari bisa hana su albashi

  • Gwamnatin Najeriya ta shiga hannun malaman jami'a, inda suka bayyana sabon kudurin yajin aiki mai dumi
  • Kungiyar malaman jami'a ta NAAT ta ce ba mambobinta sun daina aiki har sai gwamnati ta koma biyan albashi
  • Wannan na zuwa ne yayin da yajin aikin ASUU da sauran kungiyoyin ma'aikatan jami'a ke kara kamari a Najeriya

Najeriya - Ma’aikatan da ke yajin aikin a jami’o’in Najeriya, a ranar Talata sun bayyana manufar ba za su yi aiki ba matukar ba a basu albashi ba inda suka ce yajin aikin gargadi yanzu ya koma na sai baba-ta-gani.

Ma’aikatan a karkashin kungiyar malaman fasaha ta kasa (NAAT), sun ce dakunan gwaje-gwaje, wuraren bita, gonaki da sauran su za su kasance a rufe har sai gwamnati ta biya su albashi.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Daily Trust ta ruwaito cewa ma’aikatan sun bayyana raddi ne ga sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ba za a biya su albashi ba a lokacin yajin.

Yajin aiki na kara daukar sabon salo a Najeriya
Yajin aiki: Malaman jami'a sun fusata, sun caccaki Buhari bisa hana su albashi | Hoto: primestarnews.com
Asali: UGC

Da yake magana a madadinsu a Abuja, Shugaban NAAT, Ibeji Nwokoma, ya bukaci mambobinsa da su doge, kuma kada su bari dabarar “rarraba kai da mulki” na gwamnati ya rage musu kwarin gwiwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa:

“A yau an ware kungiyarmu da ASUU domin aiwatar da manufar “Babu aiki, Babu albashi”.
“Ya ku abokai, ni, shugaban ku da kuma Shugabancin kungiya na kasa muna tare da ku a wannan mawuyacin lokaci. Yajin aikin namu halastacce ne kuma yana bin kowane tsarin da ya dace.
"Saboda haka, muna tsaye kan manufar "Babu albashi, Babu aiki". Wannan tsarin raba kai da mulki na Gwamnati ba zai yi aiki ba.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

"Ku kwan da sanin cewa za mu fito da kyau, da karfi tare da kudaden da aka biya kafin ko kuma lokacin dawowa aiki. Mu kasance kai a hade, kungiyarmu ke bamu karfi."

Shugaban kungiyar ya kuma yi barazanar cewa mambobin kungiyar za su tabbatar da cewa sun ji da duk wanda ke adawa da bukatar ma’aikata a 2023.

Ya ce:

“Ina kira ga daukacin ma’aikata a Najeriya da ma’aikatanmu na NAAT da su tashi tsaye wajen ganin mun taka rawar gani a duk harkokin siyasa tare da daukar makomarmu a hannunmu."

Gwamnatin Buhari ta dauki matakin tsayar da albashin lakcarori

A baya kun ji cewa, alamu na nuni da cewa watakila gwamnatin tarayya ta aiwatar da manufar ‘ba aiki, ba albashi’ domin dakile yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dade tana yi.

Vanguard ta ruwaito cewa matakin da gwamnati ta dauka ya biyo bayan sanarwa da wasu wasiku da hukumar da ke yajin aikin ta aikewa da wasu kungiyoyin jami’o’in da suka hada da kwamitin hadin gwiwa na JAC wanda ya kunshi NASU da SSANU.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Majiyoyin da suka yi magana kan lamarin sun ce gwamnatin Najeriya ta yi amfani da manufar tsayar da albashin ne a watan Maris din 2022.

Shugaban NAAT, Ibeji Nwokoma wanda ya tabbatar da lamarin ya ce ba a biya mambobin kungiyarsa cikakken albashin su na watan Maris ba.

Ku Ba Mu N200m Cikin Kuɗin Tallafin Man Fetur, Mu Koma Aji: ASUU Ta Roƙi Gwamnatin

A wani labarin kuma, Shugaban Kungiyar malaman jami’o’i masu koyarwa, ASUU, Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana nuna halin ko-in-kula akan yajin aikin ASUU wanda hakan ya sa daliban jami’o’in Gwamnatin Najeriya suke zaune a gidajensu, rahoton The Punch.

A cewarsa, gwamnati ta kawo mafita akan kudin tallafin man fetur da kasafin Naira tiriliyan 4 amma kuma har yanzu bata ce komai ba akan ilimin jami’o’inta.

Farfesa Osodeke ya ce Naira biliyan 200 gwamnati za ta cire daga kudin kasafin tallafin man fetur, Naira Tiriliyan 4, sannan ta samu rarar Naira Tiriliyan 3.8 wurin kawo karshen matsalolin jami’o’i, Channels Television ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Malaman makarantun Poly sun bi sahu, ASUP ta sanar da shiga yajin aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel