Yanzu-yanzu: Malaman makarantun Poly sun bi sahu, ASUP ta sanar da shiga yajin aiki

Yanzu-yanzu: Malaman makarantun Poly sun bi sahu, ASUP ta sanar da shiga yajin aiki

  • Malaman makarantun Poly ASUP sun bi sahun takwarorinsu na jami'a ASUU, sun sanar da shiga yajin aiki
  • Zasu shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu kafin su shiga na din-din-din idan ba'a biya bukatunsu ba
  • Sama da watanni biyu kenan Malaman jami'a ASUU, sauran ma'aikatan jami'o'i NASU, manyan ma'aikata SSANU na yajin aiki

Abuja - Kungiyar Malaman makarantun fasaha a Najeriya ASUP ta sanar da cewa ta yanke shawaran shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu fari daga ranar 16 ga Mayu, 2022.

Punch ta ruwaito cewa ASUP ta bayyana hakan a jawabin da ta fitar ranar Laraba.

A cewar jawabin, Malaman na Poly sun yanke shawarar shiga yajin ne bayan zaman majalisar zartaswar kungiyar da akayi ranar Laraba

Yanzu-yanzu: Kungiyar Malaman makarantun Poly sun bi sahu, zasu shiga yajin aiki
Yanzu-yanzu: Kungiyar Malaman makarantun Poly sun bi sahu, zasu shiga yajin aiki
Asali: Original

Legit Hausa ta tuntubi wani dalibi mai karatu kwalejin fasaha ta jihar Kaduna watau Kadpoly, kan halin da dalibai suka shiga kan wannan sanarwa.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sam bai ji dadin labarin ba saboda suna gab da fara jarabawar karshen zango.

Dalibn wanda dan ajin karshe ne yace:
"Wannan ba karamin illata karatu na zai yi ba saboda muna shirye-shiryen zana jarabawa."
"Lokacin karshe da ASUP ta shiga yajin aiki ranar 10 ne ga Afrilu, 2021."

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) reshen kudu maso gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) wa’adin kwanaki tara su bude dukkan jami’o’in gwamnati.

Ko’odinetan shiyyar NANS ta Kudu maso Gabas, Mista Moses Onyia, ya ba da wa’adin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lillian Orji, ya fitar a madadinsa, a ranar Talata a Enugu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

ASUU, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ta tsawaita yajin aikin gargadi na watanni uku da karin wasu watanni ukun, wanda ta shiga tun a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matakin ASUU dai shi ne don matsawa gwamnati wajen biyan bukatunta da suka hada da farfado da jami'o'in gwamnati, samun alawus-alawus na ilimi da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel