Gwamnatin Najeriya Za Ta Siyo Jiragen Sama Don Yaƙi Da Wutar Daji, Ministan Harkokin Gida, Aregbesola

Gwamnatin Najeriya Za Ta Siyo Jiragen Sama Don Yaƙi Da Wutar Daji, Ministan Harkokin Gida, Aregbesola

  • Rauf Aregbesola, Ministan Harkokin Cikin Gida ta Najeriya ya ce za a siya wa hukumar kashe gobara jiragen sama don kashe gobara daga sama
  • Aregbesola ya ce bayyana hakan ne yayin taron kayyata sabon shugaban hukumar kashe gobarar ta kasa, Jaji Olola Abdulganiyu a Abuja
  • Ministan ya bukaci sabon shugaban hukumar ya mayar da hankali wurin wayar da al'umma ayyukan hukumar da kula da walwala da horas da ma'aikata

Abuja - Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana shirin siyo jiragen sama a yankunan shida na kasa ga Hukumar Kashe Gobara, FFS, domin ta rika yaki da wutan daji da sauran gobara da ke bukatar ruwa daga jirgin sama.

Daily Trust ta rahoto cewa Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wurin bikin kawata sabon kwantrola janar na hukumar kashe gobara ta kasa, FFS, Jaji Olola Abdulganiyu a Abuja.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma

FG Za Ta Siyo Jiragen Sama Don Yaƙi Da Wutar Daji, Ministan Harkokin Gida, Aregbesola
Gwamnatin Najeriya Za Ta Siyo Jiragen Sama Don Yaƙi Da Wutar Daji, Aregbesola. Hoto: Daily Trust.
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Mun fara wani tsari tare da Hukumar Sojojin Sama domin amfani da jiragen su wurin kashe manyan gobara daga sama. Ina fatan za ka karasa wannan hadin gwiwar.
"Fatan mu shine mu samu namu jiragen saman a yankuna shida na kasarnan."

Ya ce, daga yanzu, jami'an tsaro masu bindigu za su rika yi wa jami'an kwana-kwana rakiya wurin kashe gobara don kare bata gari da yan daba kai musu hari kamar yadda Information Nigeria ta rahoto.

Ministan ya bukaci CG Abdulganiyu ya dauki aikin wayar da kan al'umma domin al'umma su san cewa aikin hukumar ta FFS ba ta tsaya ga kashe gobara ba kawai.

Aregbesola ya kuma shawarci sabon kwantrola janar din ya duba batun albashi da allawus din ma'aikatansa da basu horasawa a gida da kasashen waje.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Akwai lokacin da ya bukaci kusoshin Najeriya da su yi adalci wurin caccakar gwamnatin sa, inda ya ce ba sa yaba wa mulkin sa duk da kokarin da yake yi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An damke tsohon shugaban hukumar rashawa a Kano, Muhyi Rimin Gado

Asali: Legit.ng

Online view pixel