Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma

Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma

  • Shugaban karamar hukumar Lantang ta arewa da ke jihar Filato, Ubandoma Joshua Laven, ya magantu kan harin Kanam da ke jihar
  • Laven ya ce da Gwamna Simon Lalong ya ji gargadinsa sannan ya dauki mataki da harin bai kai ga afkuwa ba
  • Harin da yan bindiga suka kai garuruwa 8 a karamar hukumar ta Kanam ya yi sanadiyar rasa rayuka fiye da guda 150

Filato - Shugaban karamar hukumar Lantang ta arewa da ke jihar Filato, Ubandoma Joshua Laven, ya yi tsokaci kan kashe-kashen kwanan nan da ya wakana a karamar hukumar Kanam na jihar.

Laven ya bayyana cewa da ace gwamnatin jihar ta karbi gargadin da ya yi mata sannan ta dauki matakin gaggawa kan rahotannin sirri, toh da an yi nasarar dakile harin, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hanzari ba gudu ba: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasan APC gwajin shan kwayoyi

Fiye da mutane 150 aka kashe sannan wasu 5,000 suka rasa muhallinsu a lokacin da yan bindiga suka farmaki garuruwa takwas a karamar hukumar Kanam.

Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma
Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Laven, wanda ya zanta da manema labarai a filin jirgin sama na Yakubu Gowon, Heipang, Jos, ya ce gwamnatin jihar ta yi kunnen uwar shegu da gargadinsa na cewa tuni yan ta’adda sun shiga dazuzzuka, tsaunuka da bayan gari da kuma kafa sansani a wasu wurare.

Ya kuma karyata fadi a wani bidiyo da ke yawo a shafukan soshiyal midiya cewa zai hana wata kabila zuwa kamfen a kasar Tarok gabannin babban zaben 2023.

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, kwamishinan labarai na jihar, Dan Manjang, ya ce ikirarin Laven hasashensa ne kawai.

Manjang ya ce gwamnati ta yi ayyuka da yawa a fannin tsaro, ko da ba a bayyana wa jama’a ba, yana mai cewa hare-haren ba wai a jihar Filato ko na kasa ba ne, illa dai a duniya baki daya.

Kara karanta wannan

Matashin da ya damfari Sarki a Kwara N33.4m, an damke shi

Laven ya ce saboda soyayyarsa ga son zaman lafiya ne ya kwato makamai fiye da 1000 a karamar hukumar Lantang ta arewa sannan ya mika su ga Gwamna Lalong, rahoton Daily Post.

Ya ce:

“Idan har zan iya kwato makamai sama da 1000 da Gwamna da sojoji suka zo nan suka karbe su, hakan ya nuna ina son zaman lafiya.
"Yanzu, suna haddasa fargaba a tsakanin al’ummata saboda wannan bidiyon makirai ne suka fassara sa."

Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan

A gefe guda, labari mai dadi daga rundunar sojin Najeriya shi ne na nasarar da suka samu a samamen da suka kai karkashin Operation Desert Sanity.

Zakakuran sojojin Najeriyan sun samu nasarar halaka mayakan ta'addanci na Boko Haram da ISWAP da ke yankin Manjo Ali Qere a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel