Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun 2 ga watan Mayu da 3 ga wata a matsayin hutun ranar ma'aikata da na sallah
  • Ministan cikin gida, Rauf Argebesola ne ya sanar da hakan ta wata takardar da ta fita ta hannun babban sakatren ma'aikatarsa, Shuaib Belgore
  • Ministan ya tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya na bada tabbacin tsare rayuka da kadarori kuma rashin tsaro ya kusan zama tarihi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 2 da 3 ga watan Mayun shekarar nan a matsayin ranakun hutun ranar ma'aikata da shagalin idin sallar azumi.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana hakan a wata takarda da babban sakataren ma'aikatarsa, Shuaib Belgore ya fitar a ranar Alhamis, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah
Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Ya jinjinawa ma'aikata kan aiki a suke tukuru, jajircewa da sadaukarwa inda yace kokarinsu yana da alaka da cigaban kasar nan da kuma mutuncin da kasar nan ke fuskanta a idon sauran kasashe.

Wani sashi na takardar ya ce "Ma'aikata na da matukar amfani. Mun kasance masu rai ne saboda muna aiki kuma matattu basu iya aiki."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoton Channels TV, Ministan ya kara da taya Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadana cike da nasara.

Aregbsola ya yi kira ga dukkan Musulmi da su yi koyi da nagartattun halayyar saukin kai, soyayya, hakuri, zaman lafiya, sadaukarwa da kyautatawa makwabta na Annabin Rahama, Annabi Muhammadu SAW.

"Ministan ya bayyana kwarin guiwarsa kan cewa kalubalen tsaro da suka addabi wasu sassan kasar nan za su zama tarihi, inda yace gwamnati tana kokari wurin ganin ta dauka matakin da'yan Najeriya za su mori zaman lafiya a koda yaushe.

Kara karanta wannan

Hotunan 'Dawafi na musamman da aka yi don Tinubu a Masallacin Harami, yace a yiwa Najeriya addu'a

“Aregbesola ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa mulkin Buhari ya mayar da hankali wurin bai wa rayuka da kadarori kariya, inda yayi kira ga 'yan Najeriya da su kasance cikin tsarin tsaron kasar nan ta hanyar kai rahoton duk wani mutum ko abu da basu yarda da shi ba ga hukumomin tsaro."

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Sanar Da Ranakun Hutun Easter Na 2022

A wani labari na daban, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Juma'a da Litinin a matsayin hutu don murnar bukukuwan Easter a kasar, rahoton Daily Trust.

Easter biki ne da mabiya addinin Kirista ke yi domin murnar dawowar Annabi Isah (AS) bayan an giciye shi kuma ya mutu.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a ranar Talata kamar yadda ita ma The Guardian ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel