Tonon silili: Bayan shiga hannu, barawo ya nuna sirrin yadda yake shiga gida ta taga

Tonon silili: Bayan shiga hannu, barawo ya nuna sirrin yadda yake shiga gida ta taga

  • Wani faifan bidiyo ya nuna lokacin da ‘yan Najeriya suka kama wani da ake zargin barawo ne da laifin kutsawa wani gida
  • An tilasta wa wanda ake zargin barawo ne ya nuna yadda ya samu shiga gidan ta wata yar karamar taga duk da kankantar ta
  • Wadanda abin ke wurin sun cika da mamaki yayin da wanda ake zargin ya haura tagar ya shiga gidan ta dan karamin ramin

Wani da ake zargin barawo ne ya nuna abin da da yawan masu amfani da shafin Instagram suka kira "tsagwaron hazaka" lokacin da aka gan shi yana shiga wani gida ta wata karamar taga.

An tilasta wa barawon ya nuna yadda ya shiga wani gini ta taga wanda aka kwatanta girmansa da ramin tattabara.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Barawo ya bayyana sirrinsa na sata
Tonon silili: Bayan shiga hannu, barawa ya nuna sirrin yadda yake shiga gida ta taga | Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Yadda ya shiga ta tagar gidan

Ga mamakin wadanda suke wurin, sai kawai suka ga mutumin ya shiga gidan yana ta rarrafe kamar maciji yana ratsawa kamar dai jarumin fim din Spider-Man.

Gani aka yi ya fara hawan bango kamar gizo-gizo, sannan ya shiga tagar da kafafunsa da farko, sannan kansa ya shiga daga karshe.

Bidiyon da aka gani a s ya sa mutane da dama sun rasa ta cewa, yayin da wasu ke bayyana shi a matsayin mutum mai hazaka.

Wadanda suke wurin sun kadu yayin da suke furta kalaman mamakin yadda mutumin ya samu shiga gidan.

An ga sarkar jami'ai a daure a hannunsa, wanda ke nuni da cewa jami’an tsaro sun shiga lamarin.

Kalli bidiyon:

'Yan soshiyal midiya sun yi martani

Kara karanta wannan

Daga cakwalkwali zuwa makaranta: Yadda Ahmed Musa ya tallafi yaro da danginsa a Legas

A halin da ake ciki, 'yan Najeriya sun shiga sashin sharhi na bidiyo a Instagram, inda suna bayyana ra'ayinsu.

Ga kadan daga cikin abubuwan da suke cewa:

@bro_jays ya ce:

"Spiderman: ban da gidana."

staqk_g yayi sharhi da cewa:

"Duk inda kai ya shige, jiki zai shiga."

@osas_khalifa yace:

"Wannan mutumin zai iya sulalewa ya shiga aljanna ba a sani ba."

@_kladcreator yayi sharhi da cewa:

"Bayan shan bugu wannan mutumin har yana karfin maimatawa."

@j27_pancakes ya ce:

"Kana iya yin duk abin da ka sanya zuciyar ka."

@oresfashioncollections ya ce:

"Me yasa kake son aikin wahala kamar wannan.. Wannan baiwar za ka iya amfani da ita wajen samun na abin ka."

Idan na daina zan mutu: Bidiyon matar da ta shekara 4 tana kwankwadar fitsarinta a madadin ruwa

A wani labarin, Carrie, mai shekaru 53 uwa ce wadda ta kirkiro wata dabi’a mai ban mamaki ta shan fitsarin da ta tsula kuma ta shafe shekaru hudu da suka gabata tana yin hakan.

Kara karanta wannan

Da wa Allah ya hada ni: Wanda aka sace ya biya kudin fansa ya hadu da wanda ya sacesa a cikin gari

Ba wai kawai tana shan fitsarin bane, tana amfani da shi a matsayin man goge hakora, tana shafa shi a karkashin idonta, sannan ta tsefe gashinta da dai sauran abubuwan kula da jiki na yau da kullum.

Da take magana a shirin TLC na My Strange Addiction, matar da ta fito daga garin Colorado a kasar Amurka ta ce yanayin fitsarin nata ya danganta da kalar abincin da ta ci a ranar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel