Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun sake kama kasurgumin dan leken asirin Boko Haram

Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun sake kama kasurgumin dan leken asirin Boko Haram

  • Rundunar sojin Najeriya ta sake kama wani kasurgumin dan ta'addan da aka dade ana nema ruwa a jallo
  • An kama Modu Babagana ne a karo na biyu bayan ya tsere a magarkamar da aka ajiye shi a shekarar 2020
  • A yanzu da aka sake kama shi, an kama shi ne lokacin da yake siyayya ga 'yan ta'addan Boko Haram

Borno - Dakarun runduna ta musamman ta 21 dake garin Bama a jihar Borno sun kama kasurgumin dan leken asiri da ake nema ruwa a jallo na 'yan ta'addar Boko Haram/ISWAP, Modu Babagana, wanda ya tsere daga hannun sojoji a garin Bama, Leadership ta ruwaito.

A cewar bayanan sirri daga Zagazola Makama, kwararre kan yaki da matsalolin tada kayar baya a tafkin Chadi, a farko an kama fitaccen dan ta'addan ne a watan Janairun 2020 da laifin aikata leken asiri kan sojoji a yankin Bama da Banki.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6

Dan leken asirin Boko Haram da aka kama
Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun sake kama kasurgumin dan leken asirin Boko Haram | Hoto: Leadership News
Asali: Facebook

Majiyar ta ce kwanaki kadan bayan an kai Babagana gidan yari, ya yi amfani da siddabaru wajen fasa gidan yari tare da kaucewa sake kamu daga sojoji.

Da aka fahimci cewa ya tsere daga hannun sojojin da ke tsare dashi a gidan yarin, sai aka bayyana cewa ana nemansa tare da yada hotunansa a kowane lungu da sako na birnin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma aka yi sa'a aka sake kama shi tare da taimakon rundunar hadin gwiwa ta farar hula a babbar kasuwar garin Bama a lokacin da yake aikin sayo kayan aiki ga ‘yan ta’adda da makudan kudade.

A yayin gudanar da bincike na farko, wanda ake zargin dan leken asirin ya amsa cewa ya kan sa ido tare da bayyana wuraren da sojoji suke da kuma motsinsu ga 'yan ta'addar.

Yan Boko Haram sun kai hari mashaya a Yobe, sun kashe 9, sun kona Kwalejin Fasaha

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Wasu yan ta'adda masu tada kayar baya da ake zargin yan kungiyar ISWAP ne sun kai hari ranar Laraba karamar hukumar Geidam a jihar Yobe kuma suka kona makarantar fasaha kurmus.

Vanguard ta ruwaito cewa cikin wadanda harin ya shafa akwai yan biyu.

Daya ya mutu kai tsaye, yayinda aka garzaya da dayan asibiti don jinya. Harin ya auku ne misalin karfe 9 na dare.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun shiga garin ne da kafa kuma suka bude wuta kuma suka bankawa kwalejin wuta. A riwayar TheCable, mutum tara yan ta'addan suka kashe.

Jami'an JTF sun damke dan Boko Haram, sun sheke 3 kan hanyar Maiduguri-Damaturu

A wani labarin, jami’an tsaron hadin guiwa, CJTF, wata kungiyar ‘yan sa kai masu taya sojoji ayyuka a arewa maso gabas, sun kama wani dan ta’adda sannan sun halaka 3 suna tsaka da satar kayan abinci a gona dake kan titin Maiduguri zuwa Damaturu.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Har Yanzu FG Ba Ta Tura Wa Ƴan Bindiga Jiragen Yaƙin Tucano Su Ragargaje Su Ba, Fadar Shugaban Ƙasa

PRNigeria ta tattara bayanai akan yadda ‘yan sa kan suka yi wa ‘yan ta’addan kwanton bauna su ka ritsa su suna sata.

Wata majiya ta sanar da PRNigeria cewa ‘yan ta’addan sun kai wa manoman farmaki a ranar Alhamis da misalin karfe 3:30pm kusa da Daiwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel