Shari'a a Najeriya: An yankewa Barawon Manja hukuncin shekaru 6 a Magarkama

Shari'a a Najeriya: An yankewa Barawon Manja hukuncin shekaru 6 a Magarkama

  • Wata kotu a jihar ondo ta ingiza geyar wani barawon jarkar manja zuwa gidan yari bayan amsa lafinsa
  • Bayanan da aka gabatar a gaban kotu sun bayyana cewa, ana tuhumarsa ne da kutsawa cikin wani gida tare da tafka sata
  • Kotu ya ingiza keyarsa zuwa magarkama, inda zai yi zaman shekara shida ko ya biya tarar N100,000

Jihar Ondo - Wata kotun majistare da ke zama a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta yanke wa Chinaza Njoku, mai shekaru 35 daurin shekaru shida a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar manja, Punch ta ruwaito.

An kama Njoku tare da gurfanar da shi a gaban kotu ne bisa laifin satar lita 25 na manja wanda kudinsa ya kai N20,000 a ranar 17 ga Afrilu, 2022, a lamba 36, ​​titin Iluyemi, cikin garin Ondo, jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Al-mundahana: EFCC ta Tsare Ɗan Tsohon Gwamnan Nasarawa kan wasu Kudade N130m

Yadda aka daure wani saboda ya saci manja
Shari'a a Najeriya: An yankewa Barawon Manja hukuncin shekaru 6 a Magarkama | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Bernard Olagbayi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya saci jarkar manja mallakin wata mata Misis Veronica Akinrinlola.

Ya kara da cewa wanda ake tuhumar ya yi amfani da makulli wajen bude kofar gidan, ya kuma shiga ya tafka sata.

A cewar takardar tuhumar, laifin ya ci karo da sashe na 412 da 390(9) na kundin laifuffuka na Cap 34 Vol.1 na Dokokin Jihar Ondo, 2006.

Mai laifin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, amma ya roki kotun da ta yi adalci kuma ta sassauta masa a hukuncin da ta yanke.

A hukuncin da ta yanke, mai shari'a, Misis Charity Adeyanju, ta samu wanda ake tuhuma da laifin sata da masu gabatar da kara suka shigar.

Kara karanta wannan

Iftala'i: Bam ya tashi a Taraba, mutane 3 sun mutu, wasu da dama sun jikkata

Don haka ta yanke masa hukuncin daurin shekaru shida a kan laifukansa na kutsawa gidan jama'a tare da tafka sata. Sai dai kotun ta ba shi zabin biyan tarar N100,000.

An gurfanar da wasu mutane biyu da laifin satar taliya 'Spaghetti'

A shari'a mai kama da wannan, an gurfanar da wasu mutane biyu Usman Yusuf mai shekaru 28 da Abdulrafiu Ashiru mai shekara 24 da ake zargin sun shiga wani shago tare da sace kwalayen taliya spaghetti na N352,000 a ranar Litinin a gaban wata kotun majistare ta Ebute Meta dake jihar Legas.

Rahoton Vanguard ya ce, wadanda ake tuhumar sun bayyana ne a kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, sata da kuma aikata laifin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya, kuma sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Insp Orobosa Osagiede, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Maris da karfe 3:00 na dare, a Iddo Plaza, Ebute Meta.

Kara karanta wannan

Wike: Idan da Ganduje ya fito takarar shugaban kasa, da tuni na janye

Osagiede ya shaida wa kotun cewa, mutanen biyu sun shiga shagon wani mutum Mista Adewale Sanusi, inda suka yi awon gaba da taliya spaghetti da ya kai kudi Naira 352,000.

Tsabar satarsa tasa mahaifinsa ya mutu, ya sake tafka sata a wajen jana'izarsa

A wani labarin, Kotun Majistare ta Ebute-Meta da ke Legas ta yanke hukuncin daurin watanni 27 ga wani korarren dan sanda, John Dennis, mai shekaru 36 da haihuwa.

An yanke masa hukuncin ne bisa laifin satar wani karfe, wanda kudinsa ya kai N6,000 a ranar da aka binne mahaifinsa da ya mutu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar mai shari'a:

“Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi kuma ya amsa laifin da ya aikata. Ya ce ya yi niyyar sayar da karfen rodin da ya sace a ranar da za a binne mahaifinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel