Harin Bam a gidan giya a Taraba: Kawo yanzu mutum 16 sun mutu

Harin Bam a gidan giya a Taraba: Kawo yanzu mutum 16 sun mutu

  • Wasu daga cikin wadanda suka jikkata sakamakon harin Bam da aka kai Taraba sun rasa rayukansu
  • Da farko da aka kai harin, mutum uku ne suka mutu kai tsaye a harim Bam da aka kai mashaya
  • Har yanzu ba'a san wadanda suka kai wannan mumunan hari ba

Taraba - Adadin wadanda suka mutu a harin Bam din da aka kai gidan mashaya a Iware, karamar hukumar Ardo-Kola ya kai 16, masu idanuwan shaida sun bayyana.

Amma kakakin hukumar yan sandan jihar Taraba, DSP Abdulahi Usman, yace mutum shida kadai suka san sun mutu.

Punch ta ruwaito cewa mutane daban-daban wanda suka hada da James Audu, Mrs. Abaagu Esther da Musa David sun bayyana cewa mutum 10 da aka kai asibiti sun mutu kawo safiyar Laraba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Taraba CP, Abimbola Shokoya
Harin Bam a gidan giya a Taraba: Kawo yanzu mutum 16 sun mutu Hoto: Punch
Asali: Facebook

Audu yace:

"Akalla mutum 16 da aka kai asibitoci daban-daban bayan harin sun mutu tsakanin daren jiya da safiyar nan."
"Sauran dake asibiti ne na cikin hali mai tsanani; addu'a muke su yi rai."

Al'ummar garin Iware sun yi kira ga gwamnatin jihar da jami'an tsaro su yi bincike don gano wadanda suka dasa Bam din.

Bam ya tashi a Taraba, mutane 3 sun mutu, wasu da dama sun jikkata

Ranar Litinin, 19 ga Afrilu, ana fargabar mutane da dama ne suka mutu sakamakon fashewar bam a garin Iware dake karamar hukumar Ardo Kola a jihar Taraba.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa bam din ya tashi ne a wani gidan giya da ke da yawan cunkoson jama’a.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan Boko Haram sun kai hari mashaya a Yobe, sun kashe 9, sun kona Kwalejin Fasaha

Sama da mutane 20 da suka hada da mata ne suka samu raunuka a lamarin. Rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da su cibiyar kula da maras lafiya ta tarayya dake Jalingo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce mutane uku sun mutu yayin da 19 suka samu raunuka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel