Haɗarin Mota: Za Mu Nakasa Tattalin Arzikin Najeriya Idan Wani Abu Ya Faru Da Jonathan, Matasan Neja Delta

Haɗarin Mota: Za Mu Nakasa Tattalin Arzikin Najeriya Idan Wani Abu Ya Faru Da Jonathan, Matasan Neja Delta

  • Kungiyar Matasan Ijaw, (IYC) ta duniya ta yi barazanar kawo cikas ga tattalin arziki matukar wani mummunan abu ya samu tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
  • An samu rahoto akan yadda ayarin motocin da suka raka Jonathan suka tafka hadari har ta kai ga hadimansa guda biyu sun rasa rayukansu a wuraren filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja
  • Ganin wannan lamarin ne ya sanya kungiyar IYC ta yi kira ga jami’an tsaro inda ta ce su yi bincike akan silar aikuwar hadarin sannan su bayyana wa duniya yadda abin ya ke

Rivers - Kungiyar Matasan Ijaw, IYC ta duniya ta bayar da sanarwa ta musamman, inda ta ce matsawar wani mummunan lamarin ya samu tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, sai ta janyo nakasu ga tattalin arziki.

Ayarin motocin da suka rako tsohon shugaban kasar sun tafka wani kazamin hadari inda wasu hadimansa masu ba shi tsaro guda biyu suka rasa rayukansu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan: Yadda ‘Yan Sandan da ke kula da ni, suka mutu nan-take a hadarin mota

Hadarin Mota: Ba Za Mu Amince a Kashe Jonathan Ba, Matasan Neja Delta Sunyi Gargadi
Hadari: Kada a halaka mana Jonathan, Matasan yankin Neja Delta sun bayyana damuwarsu. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

A wata takarda, Jonathan ya bayyana yadda suka rasa rayukansu kusa da filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Shugaban IYC na kasa ya ce jami’an da suka rasa ransu sun halaka ne yayin kare Jonathan

Yayin tsokaci dangane da lamarin, IYC ta ce jami’an tsaro su yi gaggawar bincike da kuma bayyana wa duniya asalin abinda ya janyo hadarin.

A wata takarda wacce shugaban IYC na kasa, Peter Timothy ya saki a Port Harcourt, Jihar Ribas, ya zargi wasu ne da shirya makarkashiyar halaka tsohon shugaban kasar kafin zaben 2023 ya iso.

A cewarsa, masu tsaron lafiyar nasa da suka rasa rayukansu sun kare shi ne daga harin inda ya yaba musu kwarai akan jajircewarsu.

Ya kara da cewa yankin Neja Delta da gaba daya jama’an Ijaw ba za su taba mantawa da wannan jajircewar tasu ba.

Kara karanta wannan

Ya auna arziki: Mummunan hadari ya rutsa da tsohon shugaban kasa Jonathan

Ya ce za su tayar da tarzoma idan aka halaka Jonathan

Kamar yadda ya saki a takardar:

“Alamu sun nuna ana bibiyar ran tsohon shugaban kasar. Suna son halaka shi. Kuma hakan ba ya rasa alaka da zaben 2023 na shugaban kasa dake karatowa.
“A ganin shaidanun, hanya daya ta hana shi komawa Aso Rock a 2023 shi ne halaka shi. Mun san Najeriya sarai, babu abinda ‘yan siyasa ba za su iya ba don cimma manufarsu.”

Igbifa ya ja kunne inda ya ce yankin Neja Delta da kasar Ijaw za ta tayar da gagarumar tarzoma matsawar wani abu ya samu Jonathan.

A cewarsa, Jonathan babban arziki ne ga kasar nan hakan yasa ya yi kira ga jami’an tsaro inda ya ce idan har wani abu ya samu Jonathan ba tare da sun dakatar ba, sun ji kunya.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa ta magantu

Hukumar Kiyaye Haddura, FRSC ta sanar da Daily Trust cewa ta yiwu gudun da motocin suka yi ne ya janyo hadarin.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Kwamandan FRSC na FCT, Samuel Ogar Ochi ya ce za a tabbatar an yi bincike mai tsanani akan hadarin.

A cewarsa, akwai alamun gudun da motocin suka yi ne ya janyo hadarin. Amma dai har yanzu suna ci gaba da bincike.

Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Bar Titunan Abuja Ba Har Sai An Buɗe Makarantu, 'Kungiyar NANS

A bangare guda, Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, a ranar Litinin ta cigaba da zanga-zangar ta na neman ganin an kawo karshen yakin aikin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke yi.

Da ya ke magana a yayin zanga-zangar a Abuja, shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya ce daliban a shirye suke su fito su mamaye manyan titunan Abuja, rahoton The Punch.

Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami'o'i a kasar.

Kara karanta wannan

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel