Zan Ciyo Sabon Bashi Don Cike Giɓin Da Ke Kasafin Kuɗi Shekarar 2022, Buhari Ya Faɗa Wa Majalisa
- Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga majalisar dokoki na tarayya yana neman izinin ciyo sabon bashi don cike gibin da ke kasafin kudin 2020
- A wasikar da Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya karanto a majalisar, Buhari ya ce cin bashin ya zama dole saboda sauye-sauye da aka samu a tattalin arzikin Najeriya da na duniya
- Gbajabiamila bayan karonta wasikar shugaban kasar ya mika ta ga kwamitin kudi na majalisar domin ta dauki mataki na gaba
Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga Majalisar Dokokin Tarayya yana neman a bashi damar ya ranto kudi daga kasuwannin gida Najeriya don cike gibin da ke kasafin kudin shekarar 2022.
Buhari ya bayyana hakan ne cikin wasikar da kakakin majalisar dokokin tarayya Hon Femi Gbajabiamila ya karanto yayin zaman majalisar a ranar Alhamis, rahoton Vanguard.
Shugaban kasar kuma ya bukaci a sake yin bita kan tsarin Medium-Term Expenditure Framework (MTEF) na shekarar 2022 da aka gina kasafin kudin a kanta.
"Kamar yadda ka sani Kakakin Majalisa, sabbin sauye-sauyen da aka samu da tattalin arzikin duniya da na gida Najeriya ya tilasta dole a yi garambawul ga tsarin samar da kudi da kasafin kudin 2022 ya dogara a kai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ana kyautata zaton gibin da za a samu a kasafin kudi ya karu daga Naira Biliyan 965.42 zuwa Naira Tiriliyan 7.35 wanda hakan shine kashi 3.99 cikin 100 na GDP a kasar.
"Za a cike gibin da aka samu a kasafin kudin ta hanyar ciwo sabbin bashi daga kasuwanni na gida.
"Duba da bukatar da ke akwai na yin garambawul ga kasafin kudi na 2022, ina neman hadin kan majalisar tarayya wurin ganin an amince da wannan bukatar cikin gaggawa," in ji shi.
Daga bisani kakakin majalisar ya mika wasikar ga kwamitin kudi na majalisar dokokin tarayyar domin su dauki mataki na gaba da ya dace.
2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu
A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.
Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng