Duniya juyi: Attajiran Najeriya na kara kudancewa yayin da sauran na duniya ke ganin ragi

Duniya juyi: Attajiran Najeriya na kara kudancewa yayin da sauran na duniya ke ganin ragi

  • Attajiran Najeriya na kara samun kari kan arzikinsu, yayin da na wasu kasashe ke ganin ragi karara
  • Wannan dai na zuwa ne tun farkon fara yakin Ukraine da kuma ci gaba da ganin tasirin annobar Korona
  • An samu karin sabbin biloniyoyi a duniya, amma akwai raguwar arziki a wasu bangarori na duniya

Attajiran Najeriya sun kara matsayi a cikin jerin sunayen masu kudi na duniya na Forbes na baya-bayan nan, wanda ya kunshi arzikin manyan attajirai a duniya, Channels Tv ta tattaro.

Habakar tasu ta zo ne duk da hauhawar farashin kayayyaki a duniya wanda ya haifar da girgizar tattalin arziki bayan barkewar cutar ta Korona da kuma yakin Rasha da Ukraine.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya samu karuwar arzikinsa daga dala biliyan 11.5 a 2021 zuwa dala biliyan 14 a 2022.

Kara karanta wannan

Sunaye: Jerin kasashen duniya 5 masu tarin biloniyoyin duniya

Attajiran Najeriya na kara shillawa
Duniya juyi: Attajiran Najeriya na kara kudancewa yayin da sauran na duniya ke ganin ragi | Hoto: @Adenuga @dangote @rabiu
Asali: Getty Images

Mike Adenuga, attajiri na biyu a Najeriya, ya karu daga dala biliyan 6.1 zuwa dala biliyan 7.3.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abdulsamad Rabiu, dan Najeriya na uku a jerin sunayen masu kudin kasar nan, ya ga kari a arzikinsa daga dala biliyan 4.9 zuwa dala biliyan 6.9.

Dalilin faduwar attajiran duniya da tashin 'yan Najeriya

Forbes, a takaicen takaitawa, ya ce:

"Yaki, annoba da yanayin kasuwa sun afka wa masu arzikin duniya a wannan shekara.
"Akwai 2,668 daga cikinsu a cikin jerin masu arziki na duniya a bugu na 36 na Forbes - kasa da 87 a shekara guda da ta wuce.
"Sun tara dukiya ta akallla dala tiriliyan 12.7 - dala biliyan 400 kasa da na 2021.
"Mafi girman raguwar arziki ya faru ne a Rasha, inda akwai biloniyoyi 34 da suka rage kasa da bara bayan mamayewar Vladimir Putin a kasar Ukraine, da Sin, inda gwamnati ta murkushe kamfanonin fasaha, lamarin da ya haifar da karancin biloniyoyi 87 na Sin a cikin jerin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

"Duk da haka, Forbes ta gano sama da attajirai 1,000 da suka fi arziki fiye da yadda suke a shekara guda da ta wuce.
"Kuma sabbin shiga 236 sun zama hamshakan attajirai a cikin shekarar da ta gabata—ciki har da na farko da aka taba samu daga Barbados, Bulgaria, Estonia da Uruguay.”

A kiyasinta, Amurka har yanzu tana kan gaba a duniya tare da attajirai 735 da dukiyarsu ta kai dalar Amurka tiriliyan 4.7, gami da Elon Musk, wanda ke kan gaba a jerin masu kudin duniya a karon farko.

Kasar Sin (ciki har da Macau da Hong Kong) ita ce ta biyu, tare da attajirai 607 da dukiyarsu ta kai dala tiriliyan 2.3.

A cewar Forbes:

"Mun yi amfani da farashin hannun jari da farashin musaya ne daga ranar 11 ga Maris, 2022 don kididdige kimar kudin."

Dangote ya hada N380bn a cikin wata 3, ya zarce hamshakan attajiran Rasha 4

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

A wani labarin, attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, Aliko Dangote, yanzu ya fi kusan dukkan attajiran kasar Rasha, banda hudu daga cikinsu.

A cewar jadawalin Bloomberg Billionaires Index, bakar fatar da ya fi kowa kudi a duniya a yanzu yana da kimanin dala biliyan 20 bayan da ya samu sama da dala miliyan 915 (N380.38bn) cikin watanni uku kacal.

Sabon kari na arzikin da ya samu na nuni da cewa Aliko Dangote ya zama attajiri na 79 a raye a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.