Zargin hari a Abuja: An baza sojoji a ko'ina saboda su dakile harin 'yan bindiga

Zargin hari a Abuja: An baza sojoji a ko'ina saboda su dakile harin 'yan bindiga

  • Hukumomi a babban birnin tarayya, Abuja ba su dauki lamarin tsare Abuja da sauki ba yayin da aka ji kishin-kishin za a kai hari
  • Hare-haren da kungiyoyin 'yan ta'adda ke kai wa a jihohin da ke da makwabtaka da Abuja ya sanya hukumomi cikin shirin ko-ta-kwana domin kaucewa bacin rana
  • An baza sojoji a babban birnin tarayya domin tabbatar da cewa 'yan ta'adda ba su yi barna a wurin da madafun ikon Najeriya ke da zama ba

FCT, Abuja - Wani rahoto da jaridar Daily Sun ta fitar na nuni da cewa an jawo hankalin sojojin Najeriya sakamakon rahoton sirri na wani shirin harin ta'addanci da aka shirya kai wa babban birnin tarayya Abuja.

A cewar rahoton, an tura sojoji musamman a kauyuka da kananan hukumomin dake kan hanyar Abuja/Lokoja wato Abaji, Kwali, da Gwagwalada.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Babban birnin tarayya Abuja ya cika da sojoji
Za a kai hari Abuja: An baza sojoji saboda dakile yiwuwar harin 'yan bindiga | Hoto: allnigeriainfo.ng
Asali: UGC

Tuni dai wasu daga cikin sojojin suka mika wuya tare da fara gudanar da bincike a yankin Giri da ke kusa da Jami'ar Abuja inda suka sanya shingayen bincike a duk wuraren shiga ko fita cikin birnin tarayya Abuja.

Dalilin fara wannan aikin sintiri

An tattaro cewa, biyo bayan harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja-Kaduna a ranar Talatar da ta gabata, hukumomin sojin sun yi taro tare da samar da dabarun dakile duk wani hari a birnin da jihohin da ke kewayensa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, rundunar ta kafa wani sabon atisaye mai suna Forward Operation Base (FOB) a Rijana, inda 'yan ta'addar suka dasa nakiyar IED don tashin layin dogo, kamar yadda SaharaReporters ta tattaro.

An ce sojojin na kokarin damke wasu nau'ikan motoci na musamman da kuma mutanen da ba za a iya ambata a jarida ba don gudun samun cikas ga atisayen.

Kara karanta wannan

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Atisayen da aka fara a ranar Litinin, 4 ga Afrilu ya fara samun sakamako mai kyau tare da kai wa ga kama wasu mutane.

Baya ga shingayen da jami'an tsaro ke dasa wa, sojojin na kuma gudanar da binciken kwakwaf a sassa daban-daban na birnin.

Damfara: An kama 'yar shekara 24 da ta addabi Kanawa da sata da katunan ATM

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata budurwa ‘yar shekara 24 mai suna Osasi Chinozom Juliet bisa laifin damfarar mutane ta katunan ATM din su, inji rahoton DailyTrust.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an kwato fiye da katunan ATM guda 15 daga hannun Juliet da ake zargi.

Legit.ng ta kuma tattaro cewa Juliet ta kasance cikin jerin sunayen wadanda hukumar 'yan sandan jihar Kano ke nema kafin a kama ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel