Yanzu-Yanzu: MTN, GLO, Airtel Da Sauran Kamfanonin Sadarwa Sunyi Barazanar Yin Karin Farashi

Yanzu-Yanzu: MTN, GLO, Airtel Da Sauran Kamfanonin Sadarwa Sunyi Barazanar Yin Karin Farashi

Kamfanonin sadarwa, ciki har da Globacom, Airtel, MTN da saura sun yi barazanar kara farashin kayayyakinsu idan gwamnatin tarayya bata warware matsalar da ke adabar masana'antarsu ba, rahoton Daily Trust.

Da ya ke magana a madadin kamfanonin sadarwar a Legas a ranar Alhamis, Gbenga Adebayo, shugaban kungiyar masu sadarwa ta Najeriya, ALTON, ya bawa FG wa'adin kwana bakwai.

Yanzu-Yanzu: MTN, GLO, Airtel da Sauran Kamfanonin Sadarwa Sunyi Barazanar Yin Karin Farashi
MTN, GLO, Airtel da Sauran Kamfanonin Sadarwa Sunyi Barazanar Yin Karin Farashi. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Adebayo ya ce kwace cibiyar salula a Kogi, rashin kyawun sabis a Abuja, tsadan dizel, hauhawan farashin kaya da tsare kayan sadarwa na cikin abubuwan da ke damunsu.

Shugaban na ALTON ya ce dukkan masu harkar sadarwan sun nuna damuwarsu game da rufe wuraren sadarwar a Jihar Kogi sakamakon rikicin da ya bulo tsakanin harajin da gwamnatin Jihar ke nema a hannunsu ta hannun Hukumar Karbar Haraji na Kogi, KIRS.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

"KIRS ta dauki matakin ne saboda umurnin kotu da ta samu kan zargin wasu mambobinmu da rashin biyan haraji ga gwamnatin jihar (wanda hakan ba gaskiya bane) kuma an hana mu amfani da kayayakin sadarwan da ke wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hakan na iya janyo daukewar sabis a Kogi da wasu sassan Abuja har ma da wasu sassan jihohin Nassarawa, Benue, Enugu, Anambra, Edo, Ondo, Ekiti, Kwara da Niger.
"Wadannan jihohin na da iyakoki da Jihar Kogi, a cewar shugaban na ALTON wanda kuma shine kakakin masu kamfanonin sadarwar."

Ya kuma ce hukumar cigaban Abuja, FCDA, da ofishin direktan allunan talla ba su bawa kamfanonin sadarwa damar gina wasu tashohinsu ba a Abujan.

Hakan, ya ce yana shafar ingancin sabis a Abuja da kewaye.

"Muna kira ga hukumar FCDA ta saka baki a bamu damar kawo kayayyakin aikinmu.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa: ‘Yan Majalisar Tarayya sun fusata da 'rainin wayon’ IGP da Ministocin Buhari

"ALTON da mambobinta ba za su amince da caji ba bisa ka'ida ba da ake musu. Za mu fara nazarin kudin da ake cajin kamfanonin sadarwa a wasu jihohi."

ALTON ta kuma bayyana damuwarta kan karin kudin dizel da ke kara kudin ayyuka.

Ya yi kira ga wadanda abin ya shafa su saka baki domin ganin an samu sauki a farashin na dizel.

Daga karshe ya kuma cerashin tsaro a wasu sassan kasar yasa ba su iya tura jami'ansu yin wasu ayyukan a wasu lokutan.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel