Yanzu-yanzu: Deleget din jihar Edo sun fitittiki Ministan lafiyan daga wajen taron APC

Yanzu-yanzu: Deleget din jihar Edo sun fitittiki Ministan lafiyan daga wajen taron APC

  • Bisa wasu dalilai da bamu sani ba, an wulakanta ministan lafiya, OSagie Ehanire, a farfajiyar Eagle Square
  • Yan jihar ministan, jihar Edo, dake wajen zaman deleget din jihar ne suka wulakantasa da rana tsaka
  • Cikin mamaki da borin kunya, Ehanire ya hakura kuma ya koma kusa da mataimakin shugaban kasa

Deleget din jihar Edo a wajen taron gangamin jam'iyyar APC dake gudana yau Asabar a farfajiyar Eagle Square dake Abuja sun fitittiki ministan lafiya, Dr. Osage Ehanire, daga wajen zamansu.

Har yanzu ba'a san dalilin da yasa suka koreshi daga tsakaninsu ba.

Dr. Osage Ehanire, wanda dan asalin jihar Edo ne cikin kunya tare da hadimansa ya koma wajen da manyan baki ke zaune, rahoton The Nation.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu adadin mambobin jam'iyyar APC milyan 41 a Najeriya, Mai Mala Buni

Ehanire
Yanzu-yanzu: Deleget din jihar Edo sun fitittiki Ministan lafiyan shugaba Buhari daga wajen taron APC
Asali: Twitter

Taron gangamin APC: N300 ake siyar da ruwan goran N100 a wajen taron

Farashin ruwan gora ya tashi daga N100 zuwa N300 saboda tsananin bukata a wajen taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) dake gudana yanzu haka.

Kamfanin dllancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa farashin ruwan N100 da aka sayar da safe ya tashi zuwa N300 da rana.

Wasu masu sayar da ruwan da akaji daga bakinsu sunce karancin ruwan da cin hancin yan sanda yasa suka zabga kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel