Taron gangamin APC: N300 ake siyar da ruwan goran N100 a wajen taron

Taron gangamin APC: N300 ake siyar da ruwan goran N100 a wajen taron

  • Yan kasuwa na cin karansu ba babbaka a wajen taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Yayinda ake cikin yanayi na zafi , ruwan goran da ake sayar nairaa dari ya kai har dari uku yanzu
  • Masu sayar da ruwa sun bayyana dalilan da suka sa farashin ruwa yayi tashi gwauron zabo lokaci daya

Eagle Square, Abuja - Farashin ruwan gora ya tashi daga N100 zuwa N300 saboda tsananin bukata a wajen taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) dake gudana yanzu haka.

Kamfanin dllancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa farashin ruwan N100 da aka sayar da safe ya tashi zuwa N300 da rana.

Wasu masu sayar da ruwan da akaji daga bakinsu sunce karancin ruwan da cin hancin yan sanda yasa suka zabga kudi.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Magoyin Bayan APC Ya Mutu Yayin Babban Taron Jam'iyyar a Abuja

Taron gangamin APC: N300 ake siyar da ruwan goran N100 a wajen taron
Taron gangamin APC: N300 ake siyar da ruwan goran N100 a wajen taron
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata mata mai sune Mrs Gladys Idahor tace:

"Na zo nan da motar ruwa guda da safe, amma duk na sayar."
"Na sake jido wata motar amma jami'an tsaro suka hanata zuwa. Dalilin da yasa yayi tsada kenan."

Wani mai sayar da ruwa, Mr John Dyegh, ya ce sai da suka biya yan sanda kudi kafin aka barsu su wuce da ruwa.

Yace:

"Dole mu kara kudin da muka kashe, shi yasa farashin yayi tsada."

Deleget din jihar Edo sun fitittiki Ministan lafiyan daga wajen taron APC

A bangare guda, deleget din jihar Edo a wajen taron gangamin jam'iyyar APC dake gudana yau Asabar a farfajiyar Eagle Square dake Abuja sun fitittiki ministan lafiya, Dr. Osage Ehanire, daga wajen zamansu.

Har yanzu ba'a san dalilin da yasa suka koreshi daga tsakaninsu ba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Hana Jirgin Sama Tashi a Kaduna, Sun Bindige Mutum Daya Har Lahira

Dr. Osage Ehanire, wanda dan asalin jihar Edo ne cikin kunya tare da hadimansa ya koma wajen da manyan baki ke zaune

Asali: Legit.ng

Online view pixel