Bayan shekaru hudu, kotu ta saki matar da ake zargi da kisan mijinta

Bayan shekaru hudu, kotu ta saki matar da ake zargi da kisan mijinta

  • Bayan shekaru hudu ana shari'a, kotu ta wanke matar da ake zargi da laifin aika mijinta barzahu
  • Alkalin ta kara da cewa babu hujja da ke alakanta wukar da akayi kisan da matar da ake zargi
  • A ranar 27 ga Junairu, 2017 misalin karfe 11:40 na dare aka hallaka mijinta cikin gida

Legas - Babbar kotun jihar Legas dake zamanta a Tafawa Balewa Square (TBS) ta wanke matar aure, Mary Alilu, da kisan mijinta, Kingsley Perewe, ta hanyar yi masa yankan rago.

Alkali Modupe Nicol-Clay ta saki matar auren ne wacce ta kwashe shekaru hudu a tsare kan zargin kisan, rahoton Vanguard.

Gwamnatin jihar Legas ta fara gurfanar da Mary ne ranar 12 ga Nuwamba, 2018.

Lauyoyin gwamnati Adeshola Adekunle-Bello da Titi Olanrewaju-Daud, sun bayyanawa Alkali cewa matar ta kashe mijinta ranar 27 ga Junairu, 2017 misalin karfe 11:40 na dare a gida mai lamba 111, Abukuru Street, Ajegunle, Lagos.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Dogara

Sun gabatar da shaidu uku ciki har da jami'in dan sanda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan shekaru hudu, kotu ta saki matar da ake zargi da kisan mijinta
Bayan shekaru hudu, kotu ta saki matar da ake zargi da kisan mijinta
Asali: Twitter

Alkalin kotu Nicol-Clay tace ko shakka babu an kashe mutumin, amma akwai tanakudi cikin hujjojin da shaidun gwamnati na daya da na biyu suka gabatar.

Alkalin ta kara da cewa babu hujja da ke alakanta wukar da akayi kisan da matar da ake zargi.

Tace:

"Babu wani kwakkwarin hujja da lauyoyin gwamnati suka gabatar da ya gamsar; akwai shakku da dama cikin lamarin."
"Hakazalika babu hujjar dake nuna cewa babu wani makami daban da za'a iya amfani da shi wajen kisan."
"Saboda haka an wanketa kuma an saketa."

Masu garkuwa da mutane sun halaka dan kasuwa, sun sace matarsa da yaransa

A ranar Laraba, wasu masu garkuwa da mutane sun halaka fitaccen mai saida shanu, tare da yin garkuwa da matarsa da ƴaƴansa maza a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Kwamitin bincike ya aike wa Abba Kyari sammaci, an sanar masa ranar gurfana

An tattaro yadda aka kai wa dan kasuwan, Alhaji Gidado Hassan, wanda ke shugabantar kasuwar raguna a Jalingo farmaki a gidansa dake ƙauyen Audi, misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Daily Trust ta gano yadda ƴan bindigan da za su kai sha-biyu suka kutsa cikin gidan ɗan kasuwan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel