Bidiyon tsohon gwamna yana shan ruwa cike da damuwa a ofishin EFCC

Bidiyon tsohon gwamna yana shan ruwa cike da damuwa a ofishin EFCC

  • Bidiyon gwamna Willie Obiano a ofishin hukumar EFCC yana shan ruwan gora cike da damuwa ya janyo cece-kuce
  • An kama tsohon gwamnan jihar Anambran a filin jirgin sama na Murtala Muhammad yayin da yake hanyar tafiya Houston, Ingila
  • Deji Adeyanju ya wallafa bidiyon Obiano inda ya ke shawartar masu mulki da su matukar kiyayewa yayin da suke madafun iko

Mai rajin kare hakkin da Adam, Deji Adeyanju, ya wallafa wani bidiyo na tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya na shan ruwan gora yayin da ya ke ofishin hukumar yaki da rashawa tare hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Idan za a tuna, an yi ram da tsohon gwamnan jihar Anambran a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas yayin da yake kokarin tafiya Houston, Ingila.

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

Bidiyon tsohon gwamna yana shan ruwa cike da damuwa a ofishin EFCC
Bidiyon tsohon gwamna yana shan ruwa cike da damuwa a ofishin EFCC. Hoto daga Adeyanju Deji
Asali: Facebook

Wannan kamen ya zo ne sa'o'i kadan bbayan gwamnan kudu maso gabas din ya mika mulki ga sabon gwamna Charles Soludo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adeyanjo ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook inda ya kara da tsokacin cewa:

"Tsohon gwamnan Anambra a hannun EFCC. Idan kana kan mulki, ka kiyaye."

Martanin 'yan Najeriya

Tuni 'yan Najeriya suka bi bidiyon suka fara tsokaci a kai

Abiodun Mabayomije Adenuga

"Babu wani a kiyaye yayin sata, nasihar ya dace ta kasance kamar haka "ku yi abinda ya dace yayin da kuke mulki" saboda ce wa barawo ya kiyaye yayin da yake mulki daidai yake da shawartarsa da ya kiyaye yayin sata."

Ebuka Victor Ikeakor

"Ko ma dai me yayi, ya dace a mutunta shi. Me yasa ba a wallafa irin wannan bidiyon da dan ta'addan fitaccen dan sanda mai safarar miyagun kwayoyi ba?

Kara karanta wannan

Kebbi: Mataimakin gwamna ya musanta rahoton ya jagoranci sojoji sun ragargaji 'yan bindiga

"Idan da dan arewa ko bafulatani ne, EFCC za ta iya wallafa wannan bidiyon? Ko da ya yi sata, ya dace a ga kwarewa a bangaren EFCC."

James Nelson Uche

"Kowanne gwamnan Najeriya a wani bangare ya yi barna da kudin gwamnati. Sai dai kama su ne ake zaba. Wadanda aka kama kuma a koyaushe suke fuskantar fushin hukuma ba har sai idan a su daidaita ba.
"Abun takaicin shi ne yadda mutane ke zaben wadanda suke zuwa su wawure kudin al'umma."

Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu

A wani labari na daban, dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya kuma shugaban rundunar binciken sirri, DCP Abba Kyari, ya gurfana a gaban babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kyari ya bayyana a gaban kotun tare da wasu 'yan sandan rundunar IRT da aka kama da zargin safarar hodar Iblis.

Kara karanta wannan

An yaye tubabbun yan ta'addan Boko Haram 500 da aka yiwa horo

A karar mai lamba FHC/ABJ/57/2022, an zarge su da hada kai wurin aikata laifi, kangewa da kuma harkar safarar hodar Iblis da ta kai nauyin 17.55Kg.

Asali: Legit.ng

Online view pixel