Rashin wuta, wahalar mai, ASUU da matsin lamba 6 da ‘Yan Najeriya suka shiga ciki a yau

Rashin wuta, wahalar mai, ASUU da matsin lamba 6 da ‘Yan Najeriya suka shiga ciki a yau

  • Halin da Bayin Allah su ke ciki a kasar Najeriya yana kara wahala cikin ‘yan kwanakin bayan nan
  • An dade ana fama da karancin man fetur, bayan haka kuma yanzu wutar lantarki ta gaza zama
  • A daidai wannan lokaci ne kuma ake kukan tsadar kaya, sannan malaman jami’a su na yajin-aiki

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta jero irin halin ni ‘ya sun da al’umma su ka shiga a yau:

1. Wahalar man fetur

Duk da yunkurin da NNPC ta ke yi, har yanzu man fetur bai wadaci al’umma ba. A garuruwa da-dama ana samun layin motoci a gidajen mai kafin a samu fetur.

Wani mazaunin Kano ya shaidawa ma’aikacin Legit.ng cewa ya saye litar man fetur ne a kan N250. A wasu wurare a jihar Kaduna, farashin lita ya kai N265.

Kara karanta wannan

Rashin wuta ya jawo an koma dogara da Janaretoci har a fadar Shugaban kasar Najeriya

2. Man dizil

Bayan man fetur, akwai tsadar bakin man dizil da ake fama da shi a yanzu. Rahotanni su na nuna cewa a makon nan farashin lita ya haura N720 a wasu garuruwan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan tsada ya jawo tashin kudin kaya a kasuwanni da rufe wasu masana’antun. Tun a makon da ya wuce kungiyar MAN ta fito tana kokawa gwamnatin tarayya.

3. Man jirgin sama

Yanzu haka man jirgin sama ya zama gwal a Najeriya. Kamfanonin jirage su na cewa daga ranar Alhamis (17 ga watan Maris 2022), ba su da man da za su iya tashi.

Wannan ya yi sanadiyyar tsadar farashin tikitin jirgin sama. Ana rade-radin mafi arahar tikitin jirgi da za a samu yanzu zai kai N120, 000 baya ga yiwuwar daga tafiya.

Rashin man fetur
Ana wahalar man fetur a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

4. Tsadar kaya

Alkaluma sun nuna cewa farashin kayan masarufi sun tashi a kasuwanni. Hakan yana da alaka ne da tsadar fetur da dizil wanda litarsu ya zarce N250 da N700.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

NBS ta tabbatar da kaya su na kara tsada a kasar. Legit.ng Hausa ta ji cewa Manoma su na kukan buhun taki ya doshi N20000, wanda hakan zai jawo tsadar abinci.

5. Rashin wutar lantarki

Shakka babu akwai karancin wutar lantarki yanzu a kasar nan. A makon nan an yi ta samun tangarda a tashoshin Najeriya har Minista ya kira taron gaggawa.

BBC ta ce Ministan lantarki na Najeriya, Injiniya Abubakar Aliyu ya shaida mata cewa masu fasa bututun mai ne suka taba layin gas da na’urori suke amfani da su.

6. Yajin-aikin ASUU

Duk da wadannan matsaloli kuma, malaman jami'an gwamnati su na yajin-aiki. Kungiyar ASUU ta shafe wata guda kuma za a kara watanni biyu ba a yin karatu.

Yanzu dai maganar da ake yi, Shugaba Muhammadu Buhari ya na kasar waje, shugabannin kungiyar malaman jami’ar su na zama ne da Ministocin tarayya.

Janeretoci a Aso Villa

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Dazu kun ji cewa wutar lantarki ta gagara zama, lamarin ya baci har ta kai wasu ma’aikata su na tashi daga ofis tun da rana tsaka, su tafi gidajensu a garin Abuja.

Wani ya fadawa manema labari cewa a lokacin da mutane ke kuka a kan matsalar wutar lantarki, haka abin yake a fadar shugaban kasa, da janaretoci ake amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel