Ta cika fushi: Kotu ta gimtse igiyar auren da ya kai shekaru 15 saboda yawan fushin mata

Ta cika fushi: Kotu ta gimtse igiyar auren da ya kai shekaru 15 saboda yawan fushin mata

  • Kotu ta gimtse aure tsakanin Shepnaan Emmanuel da matarsa Linda saboda yawan fushinta
  • Emmanuel ya ce baya ga yawan fadanta, matar tasa ta yi watsi da shi tsawon lokaci
  • Bisa wannan dalili ne kotu ta raba auren nasu mai shekaru 15 sannan ta mika wa mijin ragamar rike yaron da suka haifa

Plateau - Wata kotun Jos da ke zama a Kasuwan Nama, ta raba auren shekaru 15 tsakanin Shepnaan Emmanuel da matarsa, Linda, a ranar Laraba, 2 ga watan Maris saboda saurin fushinta.

A cikin karar da ya shigar, Emmanuel, ya kuma zargi matar tasa da yin watsi da shi, Vanguard ta rahoto.

Ta cika fushi: Kotu ta gimtse igiyar auren da ya kai shekaru 15 saboda yawan fushin mata
Kotu ta raba auren shekaru 15 saboda yawan fushin mata Hoto: Thisday
Asali: UGC

Ya ce ya auri Linda a shekarar 2007 sannan sun rabu a 2017 saboda dabi’arta ta yawan rigima.

Kara karanta wannan

Masoya: Ma'auratan da suka yi aure suna da shekaru 10 da 12 na ci gaba da soyewa bayan shekaru 91

Linda, wacce bata halarci zaman kotun ba, ta aike da takardar amincewarta ga bukatar mai kara na neman a raba auren ta hannun lauyanta.

Da suke zartar da hukunci, jami’an da ke jagoranci, Ghazali Adam da Hyacenth Dolnanan, sun aiwatar da bukatar ma’auratan na neman a raba auren sannan suka mika ragamar kula da ‘da daya da suka haifa a hannun Emmanue, rahoton The Eagle.

Masoya: Ma'auratan da suka yi aure suna da shekaru 10 da 12 na ci gaba da soyewa bayan shekaru 91

A wani labarin, wasu ma’aurata Yahudawa da aka haifa a kasar Yemen sun birge mutane da dama duba ga yadda suke kaunar junansu bayan shekaru 91 da aurensu.

Daga Zechariah har Shama’a duk marayu ne kuma sun yi auren wuri domin shine al’ada a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Bam ya tashi cikin dare a Kaduna – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan abin da ya auku

A shekarar 1948, ma’auratan sun yi kaura daga kasar Yemen, don guje ma kin jinin baki da kasar ke yi. Sannan suka yada zango a kasar Israila da aka kafa a lokacin. Kuma har yanzu a nan suke rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel