Masoya: Ma'auratan da suka yi aure suna da shekaru 10 da 12 na ci gaba da soyewa bayan shekaru 91

Masoya: Ma'auratan da suka yi aure suna da shekaru 10 da 12 na ci gaba da soyewa bayan shekaru 91

  • Wasu ma’aurata da suka yi aure tun suna kananan yara na ci gaba da soyewa bayan sun shafe tsawon shekaru 91 a tare
  • An yiwa Zechariah da Shama’a auren wuri tun suna da shekaru 10 da 12 domin hana su yin aure a wajen kabilarsu ta Yahudawa
  • Sai dai kuma, tun daga ranar suka fara kaunar junansu har zuwa yanzu da suka tsufa

Wasu ma’aurata Yahudawa da aka haifa a kasar Yemen sun birge mutane da dama duba ga yadda suke kaunar junansu bayan shekaru 91 da aurensu.

Daga Zechariah har Shama’a duk marayu ne kuma sun yi auren wuri domin shine al’ada a wancan lokacin.

Masoya: Ma'auratan da suka yi aure suna da shekaru 10 da 12 na ci gaba da soyewa bayan shekaru 91
Masoya: Ma'auratan da suka yi aure suna da shekaru 10 da 12 na ci gaba da soyewa bayan shekaru 91
Asali: UGC

Sun gudu daga kasar Yemen

A shekarar 1948, ma’auratan sun yi kaura daga kasar Yemen, don guje ma kin jinin baki da kasar ke yi. Sannan suka yada zango a kasar Israila da aka kafa a lokacin. Kuma har yanzu a nan suke rayuwa.

Kara karanta wannan

Abuja: 'Yan bindiga sun hallaka 'yan mata biyu a hanyarsu ta zuwa biki

Sun yi yara 11, jikoki da tattaba kunne 64

A yanzu, Zechariah da Shama’a suna da haihuwar yara 11 a tsakaninsu, sannan suna da jikoki da kuma tattaba kunne 64.

Da yake martani a wani biyo da BBC ta wallafa, Zechariah ya ce:

“Ku tuna, wannan itace mata ta farko kuma ta karshe da na aura. Kuma ba zan taba ya da ita ba.”

A nata bangaren, Shama’a ta ce:

“Ba mu lashi zuma ba a rayuwa. Babu wani azaba da ba mu dandana ba. Babu shi. Bamu da gida. Rumbun jaki muke sharewa, kuma a ciki muke zama.”

Raya Sunnah: Wani Matashi dan shekara 32 ya Auri mata uku rana daya

A gefe guda, wani matashi mai suna, Luwizo, ya Angonce da tsala-tsalan yan mata uku da suke yan uwa ɗaya a kasar Congo, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jaruma Hafsat Idris ta magantu a kan batun aurenta, hoton matashin mijinta ya bayyana

Angon ɗan kimanin shekara 32 a duniya yace ya haɗu da ɗaya daga cikin matan yan uku mai suna, Natalie, a dandalin Facebook, suka fara fira har ya kai ga soyayya.

Yace bayan sun haɗu Natalie ta gabatar da shi ga yan uwanta mata guda biyu, Nadege da Natasha, ba da jimawa ba suka faɗa soyayya da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel