‘Yan bindiga sun shigo gidan Sarki cikin dare sun yi garkuwa da Mai martaba a jihar Arewa

‘Yan bindiga sun shigo gidan Sarki cikin dare sun yi garkuwa da Mai martaba a jihar Arewa

  • Mutanen kauyen Pushit sun ga ta kansu yayin da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Mai garinsu
  • A ranar Alhamsis aka ji ‘yan bindiga sun shigo Pushit, sun yi awon-gaba da Diket Gupiya a gidansa
  • Jami’an ‘Yan Sanda da wasu mazauna wannan gari sun tabbatar da sace Mai martaba Diket Gupiya

Plateau - Hankalin Bayin Allah ya tashi a karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato bayan sace wani Basarake. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a yau.

Kamar yadda muka samu labari, ‘yan bindiga sun sace Mai martaba Diket Gupiya a Mangu.

Mai martaba Diket Gupiya shi ne mai rike da kasar Pushit. Daga wannan yanki a garin Mangu ne mataimakin gwamnan jihar Filato watau Sonny Tyoden ya fito.

Ana zargin wadannan ‘yan bindiga sun dauke Sarkin Pushit a fadarsa da ke kauyen Pushit a cikin daren ranar Alhamis din da ta wuce, 24 ga watan Fubrairu 2022.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Wata majiya ta shaidawa jaridar ta Punch cewa Diket Gupiya yana cikin gidansa yana kallon talabijin da kimanin karfe 9:00 na dare ne aka shigo masa daki.

Gwamnan Filato
Gwamna Simon Lalong Hoto: Simon Lalong
Asali: UGC

Wadannan miyagu sun kawo hari, suka kuma yi nasarar yin awon gaba da Basaraken a jiya.

‘Yan bindigan sun yi gaba da Gupiya. Kawo yanzu ba a samu wani labari a game da inda aka kai shi ba. Ana tunanin za a nemi a biya kudin fansa kafin ya fito.

Tuni dai jami’an ‘yan sanda na jihar Filato ta bakin Ubah Ogaba sun bayyana cewa sun san da aukuwar lamarin, kuma an tura dakaru domin su ceto Gupiya.

Mun shiga uku - 'Yan gari

Wani mazaunin yankin, Philip Moses ya shaidawa 'yan jarida cewa an dauke Sarkin da ya taba neman canza sunan garinsa. Newsngr ta fitar da wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna

“Abin takaici ya sake auka mana, an yi garkuwa da Cif Diket Gupiya, Mai garin mu a kasar Pushit a jiya Alhamis cikin dare.” - Philip Moses.

An kuma dauke Sarki

Ba wannan ne karon farko da aka ji irin wannan labari ba. Watanni biyu da suka wuce an ji cewa ‘yan bindiga sun sace Sarkin kasar Gundiri, Charles Mato.

Mai martaba Sum Pyem na Gundiri watau Charles Mato bai fito ba sai da aka biya kudin fansa. Wani 'danuwan Sarkin ya bada labarin abin da ya wakana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel