Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC 6, ya kuma jagoranci zaman majalisar zartarwa

Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC 6, ya kuma jagoranci zaman majalisar zartarwa

  • Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin zabe shida a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Taron rantsarwar ya samu halartan shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma shugaban INEC, Mahmood Yakubu
  • Bayan nan Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu.

Dan takaitaccen taron wanda ya gudana a zauren majalisar fadar shugaban kasa, ya samu halartan shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma shugaban INEC, Mahmood Yakubu.

Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC 6, ya kuma jagoranci zaman majalisar zartarwa
Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC 6, ya kuma jagoranci zaman majalisar zartarwa Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Kwamishinonin INEC shida da aka rantsar sune Mallam Mohammed Haruna daga jihar Neja, Misis May Agbamuche-Mbu daga Delta, Ukaegbu Kenneth Nnamdi daga jihar Abia, Manjo Janar A. B Alkali mai ritaya daga Adamawa, Farfesa Rhoda Gumus daga jihar Bayelsa da kuma Mista Sam Olemekun daga jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Babban bako a villa: Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Ghana

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Jaridar Vangurd ta rahoto cewa shugaba Buhari ya ci gaba da zaman majalisar zartarwa ta mako jim kadan bayan taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda suka hallara a taron majalisar zartarwa sune mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da babban mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

Sauran ministocin sune; ministan kwadago da diban ma’aikata, Sanata Christ Nigege, karamin ministan kwadago, Festus Keyamo, ministan kimiya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu.

Sai kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi, ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed, karamin ministan ma’adinai da karafe Uchechukwu Ogar, ministan ma’adinai Olamilekan Adegbite, ministan wuta, Jeddy Agba, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da karamin ministan kasafin kudi, Clement Agba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya

Shugaban ma’aikata Folashade Yemi-Esan da sauran ministoci sun halarci taron ne ta yanar gizo daga ofishoshinsu.

Buhari ya dage rattafa hannu kan dokar zabe zuwa ranar Juma'a

A wani labarin, mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dage rattafa hannu kan sabuwar dokar zaben Najeriya ranar Juma'a, 25 ga watan Febrairu, 2022.

ChannelsTV ta ruwaito majiya daga fadar shugaban kasa cewa da farko Buhari ya yi niyyar rattafa hannu yau Laraba, amma ya canza ra'ayinsa.

A cewar majiyar, wannan karon Shugaban kasan zai cika alkawarinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel